’Yan fashi sun yi wa motar banki luguden wuta

’Yan fashin sun yi wa motar kwanton bauna a lokacin da take hanyarta ta kai kud zuwa Warri

’Yan fashi sun yi wa motar banki luguden wuta

Diraben motar daukar kudin wani banki tare da wani dan sanda mai tsaron motar sun tsallake rijiya da baya, a wani kazamin hari da ’yan fashi suka kai wa motar.

’Yan fashin da ke dauke da muggan makaman sun bude wa motar kudin wuta ne a safiyar ranar Alhamis a yayin da ’yan sanda suke yi mata rakiya a Jihar Delta.

Wasu daga cikin ’yan fashin sun samu raunin harbi a sakamakon musayar wutar da aka gwabza tsakaninsu da ’yan sandan da ke tsaron motar.

’Yan fanhin sun kai wa motar harin kwanton bauna ne a lokacin da take hanyarta da jigilar kudi daga Asaba zuwa Warri a Jihar Delta.

Kakakin ’yan sandan jihar, Edafe Bright, ya ce ’yan fashi kusan 1o ne suka yi wa motar kwanton bauna a cikin wasu motoci biyu a kan hanyarsu ta kai kudin Warri daga Asaba.

Sai dai ya ce, “Ba a samu asarar rai ba, amma an yi wa maharan munanan raunukan harbi, abokansu suka dauke su, suka tafi da su, an kuma gano motar sannan aka kai ta wani ofishin ’yan sanda.”
Ya ce a halin yanzu rundunar ta kaddamar da bincike a kan lamarin.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu