’Yan fashi sun ziyarci hausawan Kalaba
’Yan fashi sun addabi Jihar Kuros Riba, har ta kai ga al’umma ke barci da ido daya a bude, inda ’yan fashi da makami suka yi cikin mako kacal sun harbe har mutum biyar, sai kuma uku da suka a Kalaba . Wannan matsala ta ’yan fashi da makami wutarta na ruruwa ne a daidia […]
’Yan fashi sun addabi Jihar Kuros Riba, har ta kai ga al’umma ke barci da ido daya a bude, inda ’yan fashi da makami suka yi cikin mako kacal sun harbe har mutum biyar, sai kuma uku da suka a Kalaba .
Wannan matsala ta ’yan fashi da makami wutarta na ruruwa ne a daidia lokacin da zaben kasa ke karatowa, inda a ranar Lahadin makon jiya, fataken dare suka ziyarci layin Bagobiri da ke unguwar Hausawa, cikin wata mota kirar bas, kuma yawan su ya kai kimanin shidda. Da misalin karfe tara na dare suka fara yin harbi kan mai uwa da wabi .
Muhammad Auwal Salihu, daya daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin da barayin suka kai shagon su, ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru, inda ya ce: “Muna hira ne ni da abokina bayan nagama cin abinci, sai na kashe jannareto da muke aiki da shi, na dawo bakin shago, na kwanta; sai na ga mutane sun waste, suna gudu, sai na ga mutum yana dukan gilashin kofar shagon mu, ya kamani, ya nuna mini bindiga. Domin ya ja kofar ya bude ta ki budewa, sai ya fasa gilashin kofar, ya ce in tashi in bude, sai na bude ya shigo, ya ce in tashi in ba shi abin da ke jikina, da ma Naira dubu biyu ce a jikina, sai na cire na ba shi, sai yace in kwanta.”
“ To, sai dan uwansa ya shigo suka haska da fitilar matse, da ma shagon ana dinki da kuma canji kudi, sai suka ga akwatun da ake ajiye kudi da gwala-gwalai da sauran kudi na mutane da ake ajiyewa da suka ga haka, sai suka koma suka dauko guduma suka fasa akwatunan, suka kwashe komai, suka tafi da shi. Ni daya daga cikin ’yan fashin ma sai da ya wanka mini mari, sannan suka fita suka tafi,” inji shi.
Da wakilinmu ya ji ta bakin wadanda abin ya rutsa da su, sai ya tuntubi Ibrahim Muhammad Makurdi, wato mai shagon, da aka tambaye shi ko sun sanar wa jami’an ’yan sanda lokacin da barayin suka zo, sai ya ce “ lokacin ni ba na nan, ina gida, shi ne yarana suka buga min waya, suka ce ga barayin ’yan fashi sun zo, sun yi sata a shago, amma sun yi kokarin sanar wa ’yansanda. “
Da ngane da kiyasin kimar darajar kayan da barayin suka sace masa, Ibrahim makurdi ya ce “ dukiyar ta hada da gwala-gwalai da kudin jama’a da na kasuwancin sa, duk sun hada sun kwashe a kalla kusan Naira sama da milyan daya na tafka asarar su.”
Har ilayau a satar da suka yi a unguwar, sun kwashe na’ura mai kwakwalwa da wayoyin hannu da kuma batiran wayoyi na wani mai sana’ar cajin batirin waya, inda suka yi awon gaba da su.
Aminiya ta tuntubi DSP Hogan Bassey , jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Kuros Riba dangane da matakin da suke dauka game da kazancewar fashi da makami a jihar, musamman garin Kalaba, sai ya ce a ba su hanzari, suna bakin kokari, kuma nan ba da jimawa ba, za su shawo kan matsalar .