’Yan fashin Birnin Gwari sun kashe malamin Jami’ar Kaduna
A ranar Lahadin da ta gabata ne ’yan fashin da suka addabi yankin Birnin Gwari suka harbe wani malamin Jami’ar Jihar Kaduna mai suna Malam Abubakar Abba.Majiyarmu ta ce ’yan fashin sun bude wuta ga wata motar sufuri ce da malamin ke ciki a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Birnin Gwari.Marigayin dan Babban Limamin […]
A ranar Lahadin da ta gabata ne ’yan fashin da suka addabi yankin Birnin Gwari suka harbe wani malamin Jami’ar Jihar Kaduna mai suna Malam Abubakar Abba.
Majiyarmu ta ce ’yan fashin sun bude wuta ga wata motar sufuri ce da malamin ke ciki a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Birnin Gwari.
Marigayin dan Babban Limamin Birnin Gwari ne kuma an kai wa motar hari ne da misalin karfe 5:00 na yamma.
Hankalin mutanen Birnin Gwari ya tashi sakamakon kashe malamin inda haka ya sa wasu matasan garin suka yi zanga-zangar lumana domin nuna bakin cikinsu kan irin rayukan da ake kashewa a hanyar. Matasan sun fito kan titin da misalin karfe 6:30 na safe a ranar Litinin dauke da kwalaye masu rubutun da suka hada da: “Babu tsaro a Birnin Gwari” da “Gwamna Yero muna bukatar tsaro a Birnin Gwari,” da sauransu.
Majiyoyinmu sun ce masu zanga-zangan sun tilasta wa masu ababen hawa da ke bi ta yankin canja hanya.
Hanyoyin mota da masu zanga-zangar suka tare sun hada da Birnin Gwari zuwa Funtuwa da Birnin Gwari zuwa Kaduna da Birnin Gwari zuwa Legas. Sai hanyar Kuriga da tsohon titin Birnin Gwari, kuma ba su bar titunan ba sai karfe 4:30 na yamma.
daya daga cikin masu zanga-zangar Barrista Salisu Haruna ya ce sun yi zanga-zangar ce saboda nuna bacin ransu ga kashe mutane da ’yan fashi ke yi a kan hanyar Birnin Gwari.
“Wadannan kashe-kashe na matukar damun mutanenmu, shi ya sa muka fito kan tituna domin nuna wa gwamnati cewa abin na damunmu.”
Ya ce “Bayan kashe malamin jami’ar a ranar Lahadin, ’yan fashin sun kuma shiga kauyen Kwasa-Kwasa suka yi ta ta’asarsu. Wannan ya sa muka fito domin nuna bacin ranmu a kan wannan kisa da ’yan fashi ke yi wa mutanenmu. Kuma zanga-zangar ta yi amfani domin ba mu taba dukiyar kowa ba kuma babu wanda ya ji rauni.” Ya ce akwai bukatar gwamnati ta mike tsaye wajen magance wannan masala, domin mutanen yankin tuni sun fara yanke kauna daga jami’an tsaro.
Aminiya ta fahimci ’yan sandan da aka tura wurin zanga-zangar ba su tozarta kowa ba, sai ma hakurin da suke ba matasan wanda hakan ya sa aka watse lafiya.