’Yan fashin Birnin Gwari sun kashe mutum shida
Al’ummar kauyen Ingade da ke kusa da garin Damari da ke tafiyar kilomita kadan zuwa Dogon Dawa a karamar Hukuma Birnin Gwari sun wayi gari a makon da jiya cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga da ake zaton ’yan fashi ne suka halaka mutum shida a yayin artabu da mutanen garin. Kakakin Rundunar ’Yan […]

Al’ummar kauyen Ingade da ke kusa da garin Damari da ke tafiyar kilomita kadan zuwa Dogon Dawa a karamar Hukuma Birnin Gwari sun wayi gari a makon da jiya cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga da ake zaton ’yan fashi ne suka halaka mutum shida a yayin artabu da mutanen garin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Aminu Lawan ya tabbatar da kisan, sai dai ya ce ba ya da masaniya ko yawan mutanen da aka halaka a artabu ya kai mutum shida.
Bayanan da ke fitowa daga yakin sun nuna cewa ’yan fashin ne suka auka wa garin wanda hakan ya janyo rikici har da rasa rayuka.
Haka kuma an ce a lokacin wannan artabu dukkan bangarorin sun samu raunuka da kuma asarar rayuka.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin Shugaban karamar Hukumar Birnin Gwari Alhaji Idris Musa Alhassan a tattaunawarsa da Aminiya ta wayar tarho ya ce bai san yawan wadanda aka kashe a cikin ’yan fashin ba.
“Akwai rigimar da aka yi a makon jiya a kauyen Ingade kusa da Damari a Dogon Dawa. An kashe mutum shida a Ingade a artabu da ’yan fashi. Amma ba mu san yawan wadanda suka rasa rayukansu a cikin ’yan fashin ba. Wannan yawan fashi da makami a yankin ya zama ruwan dare,” inji shi.
Shugaban ya ci gaba da cewa fashi da makami a kan titin Birnin Gwari zuwa Funtuwa ya zama ruwan dare. “Kodayake akwai fashi da makami a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtuwa da Birnin Gwari zuwa Kaduna, amma wanda aka yi a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtuwa ya fi kamari saboda kusancin hanyar da wani daji inda muke ganin a ciki ’yan fashin suke boyewa. Wasu lokutan idan suka yi fashi sukan yi wa mata fyade bayan sun karbe dukiyoyin mazajensu. Don haka sai ya ce gwamnatin na kokarin sanar da jami’an tsaro domin kawo karshen wannan matsala ta fashi da makami a kauyukan Birnin Gwari,” inji shi.
Ya bukaci jama’ar yankin su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa a yankin kuma su rika sanar da jami’an tsaro abubuwan da ba su gane ba.