’Yan fashin daji sun kashe ’yan uwan juna biyu a Kaduna
Har yanzu ana ganin motsin ’yan fashin dajin a yankunanmu.
’Yan fashin daji sun bindige wasu matasa ’yan uwan juna biyu a kauyen Gajere da ke gundumar Kutemeshi na Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a a lokacin da suke aiki a cikin gonarsu.
- An mayar da littafin da aka ara bayan shekara 65 a Amurka
- Ko hirar aikin mai dakina ba ma yi ballantana na yi mata katsalandan — Sanata Bulkacuwa
Dan majalisa mai Wakiltar Kakangi Yahaya Musa, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Kazalika, Kakangi ya ce ’yan bindigar sun kuma sace wasu manoma biyu a ranar Alhamis a garin Gwanda Mai Gyada a lokacin da suke noma.
“Eh, na samu labarin kisan domin an kira ni da safe an fada min. Bayan wadannan ma ’yan fashin dajin sun sace wasu manoma biyu a Gwanda mai Gyada a ranar Alhamis dinnan,” inji shi.
Ya ce a yanzu haka ana ganin motsin ’yan fashin dajin a yankunan Kuyello da Tabanni da Kutemeshi sai kuma Dogon Dawa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya bukaci a ba bashi lokaci ya bincika lamarin domin samun karin bayani amma har ya zuwa hada wannan lokacin.