’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas

Jami’ai sun ce an kuɓutar da tara daga cikin fasinjojin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don ceto sauran.

’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas

OOS_001

Wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun yi awon gaba da wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 a hanyar ruwa daga Bonny zuwa Okrika a Jihar Ribas.

Sai dai jami’ai a ƙaramar hukumar Bonny ta ce ta kuɓutar da tara daga cikin fasinjojin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don ceto sauran.

Shugaban Ƙaramar hukumar Bonny, Hon Anengi Barasua Claude-Wilcox ya ce, an ceto mutanen tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro.

Claude-Wilcox a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Boma Waribor ya fitar a ranar Juma’a, ya ce direban jirgin fasinja ya saɓa wa ƙa’idar wucewa ta kilomita 10, wanda haramtacciyar hanya ce ga direbobin kwale-kwalen fasinja.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Tattaunawar tsaro da shugaban ƙaramar hukumar Bonny, Anengi Barasua Claude-Wilcox ya yi, ya nuna cewa an yi fashin wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 da ke kan hanyarsa ta zuwa Bonny da yammacin ranar Alhamis a yankin Isaka da ke Ƙaramar Hukumar Okrika.

“Duk da haka, ya kamata a lura da cewa an gano mutane tara aka dawo da su Fatakwal ta hanyar sa hannun jami’an tsaro na gwamnati a kan lokaci, waɗanda a halin yanzu suka ƙara ƙaimi wajen ceto sauran fasinjoji 11.

“Ya kamata a lura cewa binciken farko ya nuna cewa, direban jirgin ya bijirewa ƙa’idar hanyar kuma ya wuce kilomita 10, hanyar ruwan da aka haramta ga direbobin Jirgin ruwan fasinjoji.