Yan fim 10 mafiya yawan mabiya a Twitter

Shafin Twitter, kafa ce da mutum zai bayyana ra’ayinsa a takaice. Idan mutum yana so zai iya sanya hotuna da bidiyo da kuma yada su ga kafafen sadarwar intanet a duk duniya. ’Yan fim din Hausa ma ba a bar su baya ba wajen wajen dafifin yin amfani da Twitter. Sai dai ba haka kawai […]

Yan fim 10 mafiya yawan mabiya a Twitter
Yan fim 10 mafiya yawan mabiya a Twitter

Shafin Twitter, kafa ce da mutum zai bayyana ra’ayinsa a takaice. Idan mutum yana so zai iya sanya hotuna da bidiyo da kuma yada su ga kafafen sadarwar intanet a duk duniya. ’Yan fim din Hausa ma ba a bar su baya ba wajen wajen dafifin yin amfani da Twitter. Sai dai ba haka kawai ’yan fim din suka rika kaura zuwa shafin twitter ba, al’amarin ya faru ne tun a farkon fitowar dandalin Facebook, inda ’yan fim da dama suka yi rububin bude turaku, sannan hakan ya ba su damar tattaunawa kai tsaye da masoyansu. Sannu a hankali suka rika zame jikinsu, musamman ma ganin yadda aka rika amfani da sunayensu wajen damfara. A bincike Aminiya, wakilinmu ya gano ’yan fim 10 mafiya yawan mabiya a twitter da kuma wainar da suke toyawa:

Ali Nuhu: Sarki ko Zaki kamar yadda ake yi wa jarumi Ali Nuhu lakabi shi ne dan fim da ya fi yawan mabiya a Twitter. Jarumin mai kimanin shekara 41, wanda ya shafe shekara 16 a harkar fim yana da mabiya 64, 411. Shi ne mai kamfanin FKD Production, wanda ya shirya fina-finai kamarsu ‘Zuri’a’ da ‘Sai Wata Rana’ yana bin mutane 1,379, inda ya bayyana ra’ayinsa sau 16, 376.
Maryam Booth: ’Yar shahararriyar jaruma Zainab Booth, ita ce ta biyu a cikin ’yan fim masu yawan mabiya a Twitter. Tana da yawan mabiya 45, 584. Ita ake wa lakabi da ‘Dijangala’ kuma tsohon Daraktan Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Malam Rabo ya taba dakatar da ita daga fim saboda a cewarsa tana da karancin shekaru. Ta yi bayyana ra’ayinta sau 5, 079, inda take bin mutane 1, 065.
Nafisa Abdullahi: Tun lokacin da ta zama jarumar fim din ‘Sai Wata Rana’ na kamfanin FKD Production ta samu dimbin masoya. Ita ce a matsayi na uku, inda take da yawan mabiya dubu 30, 111. Gwana ce waje zubar da hawaye a fim kuma ta bayyana ra’ayinta sau 2, 627, inda kuma take bin mutane 422.
Rahama Sadau: Priyanka kamar yadda ake kiran ta saboda matukar son fitacciyar jarumar Indiya Priyanka ta Indiya, ita ce a matsayi na hudu, duk da cewa ba ta dade da shigowa harkar fim ba. Tana da dimbin masoya inda ko a Twitter take da yawan mabiya. A yanzu kwamitin ladaftarwa na kungiyar MOPPAN ya dakatar da ita tsawon wata shida saboda samunta da laifin cin zarafin jarumi Adam A. Zango. Tana da mabiya dubu 27, 338, inda take bin mutane 605. Ko a lokacin zabe ta zama ’yar fim da ke bayyana sakamakon zabe a shafinta na Twitter da zarar Hukumar zabe ta sanar da sakamakon. Ta bayyana ra’ayinta hade da yada manufofinta sau 13, 001.
Sani Danja: ‘Alhaji’ shi ne sunan da mawaki kuma jarumin ke amfani da shi a Twitter. Duk da cewa Danja bai cika fitowa a fina-finai ba yanzu amma hakan bai sanya masoya harkar fim din Hausa sun manta da shi ba. Yana da mabiya 26, 701 kuma shi ne jarumin da ya fi bin mutane a Twitter da adadin 12, 277, sannan ya bayyana ra’ayinsa sau 8, 818.
Hadiza Aliyu Gabon: Ita ce a matsayi na 6, inda take da yawan mabiya 24, 034. Ta taba zama Gwarzuwar Jaruma ta Kamfanin MTN karo na biyu, ta yi bayyana ra’ayinta sau 1, 869, sannan tana bin mutane 230.
Aminu Saira: Duk da cewa jarumai sun fi yawan masoya saboda ’yan kallo fuskokinsu suke gani a fina-finai amma sanin makamar aiki a wurin Darakta Aminu Saira ta sanya yake da dimbin masoya. Masoya harkar fim sun bi shi har Twitter, inda yake da mabiya 22, 371. Ya kawo sauyin yadda ake ba da umarni a Kannywood shi ne. Yana biye da mutane 109 kacal, mafi kkaranci a cikin ’yan fim 10. Ya bayyana ra’ayinsa sau 3, 273.
Fati Washa: Fina-finai irinsu ’Ya Daga Allah’ da ‘Gaba Da Gabanta’ da sauransu sun ba ta yawan masoya, inda a yanzu take kan-kan-kan da Rahama Sadau wajen fitowa fina-finai. Tana da yawan mabiya 17, 684, ita ce ta biyu wajen bin mutane kadan bayan Aminu Saira, inda take bin mutane 138. Ta bayyana ra’ayinta sau 1, 012.
Adam A. Zango: Abin zai ba mutane mamaki idan aka ce Zango zai kasance a matsayi na tara cikin sahun ’yan fim masu yawan mabiya a Twitter. Abin ba zai ba da mamaki kasancewar ’yan watannin da suka gabata ne ya fara mu’amala da Twitter, inda wadansu suka ce yawan mabiya da ya samu a dan karamin lokaci ya nuna farin jinin da yake da shi, kasancewar idan da ya bude shafin a shekarun baya, to idan bai kasance na daya ba, ba zai wuce na biyu ko na uku ba. Yana da mabiya 11, 826, inda yake bin mutane 283, sannan ya bayyana ra’ayinsa sau 832.
Nazifi Asnanic: Shi ne mawaki kawai a Kannywood da ya samu shiga jerin ’yan fim 10 masu yawan mabiya a Twitter. A yanzu ya rikide zuwa furodusa, yana da mabiya 11, 012. Wasu mabiyansa sun ce fina-finan da ya shirya irinsu ‘dakin Amarya’ da ‘Sabon Sangaya’ da ‘Rai Da Buri’ sun kara ba shi damar tara yawan masoya ciki kuwa har da Twitter. Ya bayyana ra’ayinsa sau 184, sannan yana bin mutane 224.