’Yan fim 40 a Najeriya za su samu tallafin Naira miliyan 150

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta tallafa wa ’yan fim 40 da Naira miliyan 150 domin bunkasa harkar fim a Najeriya. An shirya kashe kudin ne a sakamakon wani tsari na tallafi ga ’yan fim da gwamnatin ta tsaro mai lakanin ‘Project ACT Nollywood.’Kamar yadda tsarin ya tanada, a za a kashe […]

’Yan fim 40 a Najeriya za su samu tallafin Naira miliyan 150
’Yan fim 40 a Najeriya za su samu tallafin Naira miliyan 150

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta tallafa wa ’yan fim 40 da Naira miliyan 150 domin bunkasa harkar fim a Najeriya. An shirya kashe kudin ne a sakamakon wani tsari na tallafi ga ’yan fim da gwamnatin ta tsaro mai lakanin ‘Project ACT Nollywood.’
Kamar yadda tsarin ya tanada, a za a kashe kudin ne wajen koya wa ’yan fim din ne yadda za su gudanar da harkokinsu da kuma dubarun sarrafa na’urorin zamani na daukar fim. Kwasa-kwasan da za a koya masu sun hada da yadda ake rubuta labarun fim, yadda ake bayar da umurni a fim, yadda ake amfani da haske a fim, yadda ake yin wasa da sauransu.
Mai ba da shawara ta musamman ga Ministar Kudi, Paul Nwabuike ya ce, an zabi ’yan fim din guda 40 da za su amfana da wannan tallafi, a sakamakon takardun bukata da suka bayar. Ya ce bayan an tantance bukatun nasu, sai aka ga cewa sun cancanta a ba su wannan tallafi, musamman ta fannin ba su horo a sana’ar tasu ta shirya fina-finai.
Kamar yadda Ministar Kudi, Ngozie Okonjo-Iweala ta ce, akwai wasu Naira miliyan 150 da aka sake warewa ga makarantu masu zaman kansu a Najeriya da suka kware wajen bayar horo ga ’yan fim. Don haka ta ce ta gamsu da yadda shirye-shryen ke gudana, kamar kuma yadda ta kara nanata cewa, ana sauraren ’yan fim su turo da takardun neman bukatar wannan tallafi, domin su ci gajiyar shirin.
“Babban kudurin shirin tallafa wa ’yan fim mai taken ‘Project ACT Nollywood’ shi ne domin a daukaka martabar harkar fim a Najeriya,” inji Ministar Kudi Ngozie. Ta kara da cewa, shirin na daya daga cikin kudurorin Shugaba Jonathan na bunkasa harkar fim a Najeriya. A makon da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta tallafa wa ’yan fim 40 da Naira miliyan 150 domin bunkasa harkar fim a Najeriya. An shirya kashe kudin ne a sakamakon wani tsari na tallafi ga ’yan fim da gwamnatin ta tsaro mai lakanin ‘Project ACT Nollywood.’
Kamar yadda tsarin ya tanada, a za a kashe kudin ne wajen koya wa ’yan fim din ne yadda za su gudanar da harkokinsu da kuma dubarun sarrafa na’urorin zamani na daukar fim. Kwasa-kwasan da za a koya masu sun hada da yadda ake rubuta labarun fim, yadda ake bayar da umurni a fim, yadda ake amfani da haske a fim, yadda ake yin wasa da sauransu.
Mai ba da shawara ta musamman ga Ministar Kudi, Paul Nwabuike ya ce, an zabi ’yan fim din guda 40 da za su amfana da wannan tallafi, a sakamakon takardun bukata da suka bayar. Ya ce bayan an tantance bukatun nasu, sai aka ga cewa sun cancanta a ba su wannan tallafi, musamman ta fannin ba su horo a sana’ar tasu ta shirya fina-finai.
Kamar yadda Ministar Kudi, Ngozie Okonjo-Iweala ta ce, akwai wasu Naira miliyan 150 da aka sake warewa ga makarantu masu zaman kansu a Najeriya da suka kware wajen bayar horo ga ’yan fim. Don haka ta ce ta gamsu da yadda shirye-shryen ke gudana, kamar kuma yadda ta kara nanata cewa, ana sauraren ’yan fim su turo da takardun neman bukatar wannan tallafi, domin su ci gajiyar shirin.
“Babban kudurin shirin tallafa wa ’yan fim mai taken ‘Project ACT Nollywood’ shi ne domin a daukaka martabar harkar fim a Najeriya,” inji Ministar Kudi Ngozie. Ta kara da cewa, shirin na daya daga cikin kudurorin Shugaba Jonathan na bunkasa harkar fim a Najeriya.