’Yan fim da mawaka na Kudancin Najeriya sun jajanta wa wadanda harin bam din Abuja ya jikkata
A farkon makon nan ne ’yan fim da wasu mawaka da suka fito daga Kudancin Najeriya suka shiga sahun al’umma da suke jajantawa da tallafa wa mutanen da harin bam din da ya faru a garin Nyanya, Abuja a kwanakin baya ya jikkata.’Yan wasan fim da suka hada da Genebiebe Nnaji da Rita Dominic da […]

A farkon makon nan ne ’yan fim da wasu mawaka da suka fito daga Kudancin Najeriya suka shiga sahun al’umma da suke jajantawa da tallafa wa mutanen da harin bam din da ya faru a garin Nyanya, Abuja a kwanakin baya ya jikkata.
’Yan wasan fim da suka hada da Genebiebe Nnaji da Rita Dominic da Emem Isong da Omoni Oboli da sauransu, sun nuna alhini da bakin cikinsu game da wannan harin bam da aka kai garin Nyanya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da saba’in, wasu kuma sama da dari suka samu muggan raunuka da asarar dukiya. A Litinin da ta gabata ce ’yan wasan suka rika furta alhinin nasu ta kafofin watsa labarai daban-daban, musamman ma ta turakunsu na intanet, kamar Twitter, Facebook da Instagram da sauransu.
A nasa bangaren, shi kuwa shahararren mawakin zamani daga Kudancin Najeriya, Iyanya, ya share kwanukan karshen makon da ya gabata ne a Abuja, inda ya ziyarci majinyatan da ke kwance a asibitoci daban-daban, inda ya jajanta musu.
A kwanakin bayan ne mawakin ya kaddamar da wata gidauniya domin tallafa wa marasa galihu, don haka a lokacin da ya ziyarci majinyatan, ya bayyana wa al’umma cewa ziyarar majinyatan ta kasance daya daga cikin ayyukan da gidauniyar tasa ta fara aiwatarwa.
Haka shi ma wani fitaccen mawakin, Dapo Oyebanji, wanda aka fi sani da lakanin D-Banj, a Talatar da ta gabata ya ziyarci majinyatan, inda ya yi kira ga matasan Najeriya da su guji tada zaune tsaye, su kasance masu son zaman lafiya.
“Ni dan Najeriya ne kuma duk wata annoba da ta shafi mutanen kasar nan, ni ma ta shafe ni, musamman ma a wannan lokaci da ake bukukuwan Ista. Na zo ne domin in jajanta wa wadanda wannan hari ya samu.” Inji D-Banj.
Ya kara da cewa: “Na gana da wadanda suka tsira daga harin kuma suke jinya a halin yanzu. Suna murmurewa sosai, don haka godiya ga kwararrun malaman asibiti da suke aikinsu yadda ya dace.”
Da ya koma kan wadanda ke tayar da bama-baman kuwa, D-Banj ya ce: “Muna roko ga masu kashe al’umma da su sake tunani, su maida hankali wajen tattaunawa domin zaman lafiya ta yadda al’ummarmu za su kubuta daga wannan keta.”
Wasu mutane kuwa yabawa suka yi da yadda ’yan fim da mawakan na Kudancin Najeriya suka jajanta wa majinyatan, ba kamar yadda takwarorinsu na Arewa ba da suka nuna halin ko’inkula da al’amarin.