’Yan fim din da suka samu sa’a

Wasu daga cikin masu gudanar da sana’ar fim, ba su samu nasara cikin sauki ba, wasu ma haka suka fara, kuma suka kare ba tare da sun tsinana komai ba. Wasu kuwa cikin kankanen lokaci suke zama masu nasara, inda a baya suke cikin talauci. Wasu daga cikin ’yan fim na duniya da suka samu […]

’Yan fim din da suka samu sa’a

Wasu daga cikin masu gudanar da sana’ar fim, ba su samu nasara cikin sauki ba, wasu ma haka suka fara, kuma suka kare ba tare da sun tsinana komai ba. Wasu kuwa cikin kankanen lokaci suke zama masu nasara, inda a baya suke cikin talauci. Wasu daga cikin ’yan fim na duniya da suka samu nasarar zama hamshakan attajirai, alhali a can baya ba su da komai sun hada da Jennifer Aniston da Jonny Depp da Megan Fod. Sauran sun hada da mawakiya Beyonce da dan fim Brad Pitt da kuma mawakiya Madonna.
Ita dai Jennifer Aniston, a can baya tana aikin tallar kan tarho ne, ba ta mallaki wata dukiya ta a zo a gani ba, sai da Rachel Green ya sanya ta cikin fim din F.R.I.E.N.D.S, inda tun daga lokacin tauraruwarta ta haska. Shi kuwa Johnny Depp, a can baya yana sana’ar sayar da alkalami ne, kafin Nicholas Cage ya sanya shi cikin fim din Captain Sparrow.
Shi kuwa Megan Fod, bai da wani aiki a can baya sai rarraba takardu a shagon sayar da kayayyaki. Ita kuwa Beyonce, a can baya aikinta shi ne shara a shagon kisto kuma tana sayar da gashi, amma ga shi yanzu ta zama hamshakiyar mawakiya, mai dukiya. Shi kuwa Brad Pitt, a baya direba ne shi. Ita kuwa Madonna, kafin ta fara waka, ita ma’aikaciya ce a shagon sayar da kayayyaki.
A yanzu al’amuran wadannan ’yan fim da mawaka sun zama tarihi, domin kuwa sun gamu da gyadar dogo, sun zama hamshakan attajirai.