’Yan fim mu gyara dabi’unmu- Sadiya Zo-Ki-Ji

Sadiya Abubakar  fitacciyar jaruma ce. A hirar da ta yi da Aminiya ta bayyana yadda ta fara harkar fim da nasarorin da ta samu a harkar da kuma wasu daga cikin kalubalen da ta fuskanta: Tarihina a takaiceAssalamu alaikum, sunana Sadiya Abubakar, amma an fi sani na da Sadiya Zo-Ki-Ji. An haife ni a Unguwar […]

’Yan fim mu gyara dabi’unmu- Sadiya Zo-Ki-Ji
’Yan fim mu gyara dabi’unmu- Sadiya Zo-Ki-Ji

Sadiya Abubakar  fitacciyar jaruma ce. A hirar da ta yi da Aminiya ta bayyana yadda ta fara harkar fim da nasarorin da ta samu a harkar da kuma wasu daga cikin kalubalen da ta fuskanta:

Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Sadiya Abubakar, amma an fi sani na da Sadiya Zo-Ki-Ji. An haife ni a Unguwar Rimi da ke Kaduna a shekarar 1990. Na yi makarantar firamare da sakandare  a Unguwar Rimi. Na yi Difloma a kan aikin jarida a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 2007.
Dalilin da ya sa na shiga harkar fim
Sha’awa ce wadda ta samo asali tun lokacin da nake karama,  ba na manta yadda muke shaukin kallon fina-finan Indiya da wasu daga cikin fina-finan Hausa na farko-farko kamar su ‘Daskin Da Ridi’ da ‘Sangaya’ da ‘Mujadala’ da sauransu.
Fina-finan da nake ciki
Na yi fina-finai kusan 100, a ciki akwai ‘Mai Shinku’ da ‘Zo Ki Ji’ (wanda sunansa ya bi ni) da ‘kangin Bauta’ da ‘Halina’ da ‘Jari Hujja’ da sauransu.
Jarumin da na fi so mu fito a fim tare
A gaskiya na fi son fitowa tare da jarumai kamarsu Ali Nuhu da Sani Danja da kuma Shu’aibu Lawal (Kumurci). Sai kuma bangaren jarumai mata, ina jin dadin aiki tare da Fati Ladan da Fati KK da kuma Zainab Indomie.  
kallon da ake yi wa ’yan fim mata
Tabbas, akwai wasu matan da suka kasance bata gari ne a harkar. Amma ba a taru aka zama daya ba. Akwai na kirki da na banza. Saboda haka ne ma ya sa ya dace mu gyara dabi’o’inmu.
kalubale
A gaskiya na fuskanci kalubale daga gida a lokacin da aka fahimci cewa na shiga sana’ar fim. Da farko iyayena ba su ba ni goyon baya ba. Sai da ta kai ga na gudu zuwa Kano wajen yayar mahaifiyata. Ko da na bayyana mata bukata ta, sai ta ba ni dukkan goyon bayan da ya dace don shiga harkar fim. Amma ba ta bar ni haka nan ba, sai da ta ba ni sharadin cewa in tsare mutuncina da na addinina.
Nasarori
Albarkacin sana’ar fim na sauke farali, na gina gida na kuma kai mahaifiyata Ummura. Na kuma yi suna Gabas da Yamma, Kudu da Arewa.
Burina
Babban burina shi ne na samu miji in yi aure. Wani burina kuma shi ne, Allah Ya ba ni ikon bin iyayena sau-da-kafa.