‘Yan fim sun samu tallafin Gwamnatin Tarayya ta hanyar shirin Sure-P

Kamfanoni goma masu shirya fina-finan Hausa da ke Jihar Kano ne suka samu shiga tsarin bayar da horo na gwaji (Pilot project) a karkashin shirin da Gwammnatin Tarayya ta fito da shi na samar da ayyukan yi ta hanyar koyon sana’o’i domin dogaro da kai, a karkashin Hukumar SURE-P, mai tattalin kudaden tallafin da aka […]

‘Yan fim sun samu tallafin Gwamnatin Tarayya ta hanyar shirin Sure-P

Kamfanoni goma masu shirya fina-finan Hausa da ke Jihar Kano ne suka samu shiga tsarin bayar da horo na gwaji (Pilot project) a karkashin shirin da Gwammnatin Tarayya ta fito da shi na samar da ayyukan yi ta hanyar koyon sana’o’i domin dogaro da kai, a karkashin Hukumar SURE-P, mai tattalin kudaden tallafin da aka janye na man fetur.

Mataimakin Shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa Film Makers Association of Nigeria, Malam Salisu Mohammed ne ya ce hakan ne a lokacin da yake bayyana wa Aminiya irin nasarorin da kungiyarsu ta samu a ofishinsa a Kano.
Ya ce, an zabi wadannan kamfanonin ne don su ba da horo a kan wasu fannoni na aikin shirin fim wadanda suka hada da rubuta labari da tsarawa da shiryawa da ba umarni da daukar hoto mai motsi (bideography) da samar da sutura da kwalliya da yadda ake gina dandalin daukar fim (set design and construction) da sauransu.
Kamfanonin za su bayar da horon ne ga matasa wadanda hukumar ta tantance, ta kuma turo su kamfanonin.
Hukumar ce za ta biya kamfanonin ladan bayar da horon, ta kuma ba da alawus ga wadanda za a horar a yayin da ake horar da su.
Tuni dai jami’an Hukumar SURE-P suka zo Kano inda suka tantance wadannan kamfanoni, za kuma a fara wannan aikin horarwa nan ba da dadewa ba.
A cikin kamfanonin da aka zaba akwai Mandawari Enteprises da Allyman Media da Kumbo Productions da Iyan-tama Multimedia da Gwanja Productions da Dabo Tb Center da sauransu.