’Yan fim za su je kwas Indiya

Likkafar ‘yan fim din Hausa a kullum kara gaba take, hakan ne ya sa a watan gobe za su je kwas Indiya kan aikin fim da suka hada da dabarun aktin da daukar fim da kuma sabbabin hanyoyin daraktin.‘Yan fim din za su je kwas din Indiya ne karkashin Gwamnatin Tarayya a shirinta na Nollywood […]

’Yan fim za su je kwas Indiya

Likkafar ‘yan fim din Hausa a kullum kara gaba take, hakan ne ya sa a watan gobe za su je kwas Indiya kan aikin fim da suka hada da dabarun aktin da daukar fim da kuma sabbabin hanyoyin daraktin.
‘Yan fim din za su je kwas din Indiya ne karkashin Gwamnatin Tarayya a shirinta na Nollywood Project Act, wadda ta kirkiro don tallafa wa masana’antar fim a Najeriya.
A yanzu dai shirye-shirye sun yi nisa inda aka sa ranar 28 ga watan goben a matsayin ranar tafiya.
Shugaban kungiyar Arewa Filmmakers of Nigeria, reshen Jihar Kano ya tabbatar da tafiyar, inda ya ce sun mika wa Gwamnatin Tarayya sunayen mutane 21 kuma mafi yawansu daraktoci ne.
Ya ce: “Tabbas shirye-shirye sun yi nisa, har an sanya ranar 28 ga watan gobe a matsayin ranar tafiya, kuma kungiyar Arewa film Makers Association of Nigeria ta mika wa gwamnatin tarayya sunayen wadanda za su je kwas din Indiya, amma daraktoci sun fi yawa.”
Ya ce za a shafe wata daya ne yayin kwas din.
A binciken da Aminiya ta gudanar ta gano a cikin sunayen da Arewa ta mika wa Gwamnatin Tarayya akwai: Hamisu Iyantama da Ali Nuhu da Mustafa Musty da darakta  Hafizu Bello da Mika’ilu bin Hassan Gidigo da Aminu Saira da Falalu dorayi da Bashir Rijau daga Abuja. Cikin forudusoshi kuwa akwai Baba karami da Isma’ila Na’Abba Afakallah da Ahmed Biffa da Salisu Mohammed Officer da Mohammed Sani Katsina da kuma Habibu Barde. A cikin mata akwai Hauwa Maina da sauransu.  
Mataimakin Shugaban kungiyar Arewa Film Makers, Malam Salisu Mohammed Officer ya ce a karkashin wannan shiri na Gwamnatin Tarayya za a tura mutane 40 zuwa kasar waje don yin kwas a kan harkar fim domin su kara gwanancewa a shirin fim, “20 daga kudu; 20 daga Arewa. ’Yan fim din kudancin Najeriya sun dade da mika sunayen wadanda za su yi kwas din a kasar Amurka. ‘Yan fim 20 daga Arewacin kasar nan kuma za su samu nasu kwas din ne a Indiya. Tuni dai Arewa ta bayar da sunayen mutane 20 cikin mambobinta don cin gajiyar wannan kwas din wanda ake sa ran farawa a cikin watan gobe.”
Idan ba za a manta ba dai a baya an shirya zuwa wata makaranta a kasar Amurka mai suna New York Film Academy, inda har wadanda aka bayar da sunan nasu suka bayar da Dala 50, kimanin Naira 8,450 a matsayin kudin form din shiga makarantar, amma daga baya aka karkata akalar karatun zuwa kasar Indiya wata kila saboda alakar fina-finan Hausa da Indiya.