‘Yan fim za su yi Maulidi a Kano
Yan fim karkashin kungiyar Arewa Film Makers Association of Nigeria za su gudanar da maulidi a Kano.Za a gudanar da bikin maulidin ne jibi Lahadi a Social Welfare da ke titin Court Road da misalin karfe 2:00 na rana. Shugaban kungiyar na Jihar Kano Isma’il NaAbba Afakallah ya ce ba wannan ne lokaci na farko […]
????????????????????????????????????

Yan fim karkashin kungiyar Arewa Film Makers Association of Nigeria za su gudanar da maulidi a Kano.
Za a gudanar da bikin maulidin ne jibi Lahadi a Social Welfare da ke titin Court Road da misalin karfe 2:00 na rana.
Shugaban kungiyar na Jihar Kano Isma’il NaAbba Afakallah ya ce ba wannan ne lokaci na farko da suka fara shirya bikin Maulidi ba kasancewar sun yi a bara.
“A matsayin mu na ‘yan fim Musulmi muna da rawar da za mu taka wajen nuna soyayyarmu ga zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annnabi Muhammadu (SAW). Wannan maulidin zai kara hada kan ‘yan fim.” Inji Afakallah.
Malaman da aka gayyata sun hada da Khalifa karibullah Nasiru Kabara da Malam Ibrahim Khalil da sauransu.