’Yan ‘gaban goshin’ Tinubu da suke damawa a sha haka a Nijeriya
Har yanzu Faleke na ci gaba da zama cikin ’yan gaban goshi da ke fada-a-ji a gwamnatin Tinubu.
Daga dawowar Nijeriya turbar dimokuradiyya a 1999 zuwa yanzu an yi shugabannin kasa guda biyar kuma kowane da irin salon mulkinsa wanda ke da tasiri da irin mutanen da ke kewaye da shi.
Farawa daga tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa da Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari zuwa kan Shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu, kowanensu na da ’yan gaban goshi ko ’yan lele a fadarsa da suke taka rawar da ta yi tasiri wajen sa a yi ko a bari.
- Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba — Gwamnoni
- An kashe ’yan sanda 7 da wasu 35 a Zamfara da Katsina
Wadannan mutane sun kunshi iyalai kamar kan matan aure da ’ya’ya da abokai da manyan ’yan jam’iyya a jiha da tarayya da wakilan Majalisar Zartarwa da na Majalisar Dokoki ta Kasa.
Masu sharhi a kan al’amura a lokuta da dama sun bayyana rawa da tasirin da Hajiya Turai ’Yar’aduwa da Dame Patience suka taka a kan shugabancin kasar nan tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015 lokacin mulkin mazansu.
Haka abin yake ga Ambasada Babagana Kingibe, mai shekara 78 da ya yi aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya lokacin gwamnatin ’Yar’aduwa wanda ake lissafawa cikin masu karfin fada-a-ji na Shugaban Kasar.
Kingibe, wanda masanin harkokin diflomasiyya ne, dan siyasa kuma ma’aikaci, ya rike manyan mukamai da dama a kasar nan tun daga shekarun 1970 kuma ya yi aiki da shugabannin kasa guda shida hatta a lokacin Buhari da ana lissafa shi cikin ’yan gaban goshin Shugaban masu karfin fada-a-ji.
Kingibe, wanda ya yi takarar Mataimakin Shugaban Kasa tare da Cif Moshood Abiola a zaben 1993 da aka soke, Shugaba Buhari ya sanya shi cikin tafiyarsa inda ya nada shi Wakili na Musamman kan yankin Tafkin Chadi da Kasar ta Chadi.
Shi da marigayi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari da Mamman Daura, wani da ga Buhari da wasu, sun taka muhimmiyar rawar a lokacin mulkin Shugaba Buhari.
A daidai lokacin da shugaba Tinubu ke cika shekara guda a shugabancin Nijeriya wasu sababbin zubin ne ke damawa a sha yadda suka so kamar dai a gwamnatocin da suka gabata.
Wannan rubutun zai tabo wasu mutane ne a gwamnatin Tinubu da ake jin su ne ’yan gaban goshi wadanda da bazarsu ake taka rawar tafiyar da gwamnatin.
Femi Gbajabiamila
Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Gbajabiamila, na hannun damar Shugaba Tinubu ne da yake ji da shi.
Sun fito jiha daya da Tinubu kuma wanda Tinubun ke mara masa baya tun 2003, lokacin da aka fara zabarsa zuwa Majalisar Wakilai a karo na farko don wakiltar Mazabar Surulere da ke Jihar Legas inda aka ci gaba da zabarsa har karo shida.
Dan siyasar kuma lauya, Gbajamiamila na kare ubangidansa da karfin ikonsa a majalisa a lokacin zabe, kafin da bayan zabe, inda ya ci gaba da tallata shi, abin da ya sa ’yan Nijeriya da dama ba su yi mamakin nada shi a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ba.
Ana ganin tasirin Gbajabiamila na daga cikin abin da aka yi amanna da shi wajen ba shi wannan matsayi da ke kula da kusan dukkan wasu kusoshin da ke aiki a fadar da kuma aikin bayar da umurni da zartar da manufofin Shugaban Kasa zuwa ga Sakataren Gwamnati da Babban Hafsan Tsaro da sauran manyan kusoshin gwamnati da kuma jagorantar duk wata zama da manyan kusoshin da ke aiki a fadar Shugaban Kasar da sauransu.
Hakika wadannan ayyuka sun ba shi cikakken karfi da dimbin iko a matsayinsa na Shugaban Ma’aikata, kuma mutanen da suke kusa da fadar sun ce yana amfani karfinsa yadda ya kamata.
Cif Bisi Akande
Tsohon Gwamnan Jihar Osun kuma Shugaban Riko na farko na Jam’iyyar APC, tsohon aminin siyasa ne na Shugaban Kasar.
Dattijon wanda ya yi Gwamna a karkashin Jam’iyyar AD, ‘mashawarci ne na bayan fage’ ga Shugaban Kasar.
Aminin Tinubu ne, da tun kafin zabe Tinubu yakan ziyarci Shugaba Buhari tare da Bisi Akande, wanda shi Buharin yake girmamawa, saboda rawar da ya taka wajen hadakar jam’iyyun CPC da ANPP da wani bangare na APGA don kafa Jam’iyyar APC.
Wasu masu sharhi sun ce da dama daga masu son ganawa da Shugaba Tinubu sukan yi kamun kafa ne da Akande.
An jiyo shi yana fada a lokacin da ya fara kai wa Tinubu ziyara ranar 12 ga watan Yunin 2023 cewa, “A duk lokacin da muka ji wani korafi, to lokaci ya yi da za su bai wa Shugaban shawara.”
Tinubu da Akande sun kasance a fagen siyasa daya tun daga 1999 har 2003.
James Abiodun Faleke
Faleke ne Sakataren Kwamitin Yakin Zaben Tinubu a Jam’iyyar APC a zaben da ya gabata.
Haifaffen Jihar Kogi, kuma gaban goshin Tinubu ne da ya taka muhimmiyar rawa wajen yi masa kamfe.
Ya kasance a Majalisar Wakilai inda yake wakiltar Mazabar Ikeja a Legas tun shekarar 2011.
Shi ne wanda aka sa ran zai zama Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa kafin a ba Gbajamiamila.
Mai shekara 64 kwararren dan kasuwa ne mai bayar da sahawarwari kan kasuwanci kuma dan siyasa, inda ya fada harkokin siyasa gadan-gadan a shekarar 2003, bayan Tinubu ya nada shi a matsayin Babban Sakataren sabon Yankin Raya Kasa na Ojodu (LCDA) lokacin yana Gwamnan Jihar Legas inda ya shugabance ta har karo biyu a tsakanin Nuwamban 2003 da Afrilun 2004, sai aka zabe shi Shugaban LCDA nan ma ya shugabance ta sau biyu zuwa karshen 2011.
An ce Tinubu ne ya goya masa baya a takarar da ya yi Mataimaki ga marigayi Yarima Abubakar Audu a zaben 2015 a Jihar Kogi.
Shi kansa Abubakar Audu na dasawa da Tinubu. Sai dai bai samu damar darewa kujerar Gwamnan Kogi ba lokacin da aka sanar da rasuwar Abubakar Audu gab da za a sanar da sakamakon zaben.
Har yanzu Faleke na ci gaba da zama cikin ’yan gaban goshi da ke fada-a-ji a gwamnatin Tinubu.
Sanata Oluremi Tinubu
Ita ce Uwargidan Shugaban Kasa Tinubu, wadda shawarwarinta ba abin yadawa ba ne.
Ita ce ta kafa Kungiyar Renewed Hope Initiatibe (RHI) kuma ’yar siyasa ce ta gidi sannan kashin-baya a takarar mijinta Tinubu tun gwamman shekaru da suka wuce.
Sanata Remi ta kasance mai kare muradun mata da kananan yara, inda take amfani da kungiyarta ta RHI wajen tallafa wa mata da marasa galihu da fuskar noma da ilimi da kiwon lafiya da kuma jarin kasuwanci.
Duk da halin matsi da ake ciki, takan kai tallafi ga ’yan kasa a yayin da take zagayawa don gudanar da wasu harkokin a fadin kasar nan.
Mai shekara 63 a duniya, Remi ta wakilci Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattijai tun daga 2011 har zuwa 2023.
Ta kasance ’yar Jam’iyyar APC mai ra’ayin kudirorin mijinta. Tasirinta a harkokin jam’iyya da mulkin mijinta abu ne da ba za a yi kowanto ba, a matsayinta ta babbar ’yar siyasa.
Seyi Tinubu
Seyi, dan Shugaban Kasa Tinubu shi babban wakili ne kuma abokin hadin gwiwa wajen kafa Kungiyar TELD NGO da aka kaddamar a shekarar 2005, da niyyar inganta rayuwar marasa galihu ta hanayr bayar da tallafi da shirye-shiryen koyarwa.
Lauya ne da ya yi digiri na daya a fannin lauya da digiri na biyu a fannin dokokin kungiyoyi da harkokin kasuwanci a Jami’ar Buckingham da ke Ingila, inda ya halarci Makarantar Kwarewa a Aikin Lauya ta Nijeriya a shekarar 2013, yana sahun gabagaba wajen yi wa mahaifinsa kamfe a zaben da ya gabata.
Masu sharhi sun ce yana fafutika ne don matasa a gwamnatin mahaifinsa kamar yadda ya jagoranci neman goyon bayansu don mara wa mahaifinsa a zaben 2023.
Kafin tsohon Shugaban Kasa Buhari ya sauka daga mulki, Seyi ya jagoranci wani ayari na Kwamitin Kamfe na Tinubu/Shettima suka kai masa ziyarar ban-girma a gidansa na Daura a Jihar Katsina a Disamban 2022, inda suka nema wa mahaifinsa goyon baya.
Hotunan ziyarar sun nuna yadda ayarin suke gai da Buhari, yayin da Seyi ya durkusa.
Sai dai masu sharhi sun ce mahaifinsa ya dasa aya ga tasirinsa, bayan da a watan Oktoban 2023 ya gargade shi tare da wasu kan shiga zauren taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC).
Shugaban ya ce ya lura da shige-da- ficen mutanen da ba su da izini a wajen taron majalisar na mako-mako da ake yi don tattauna muhimman ala’muran da suka shafi kasa.
Ya yi gargadin cewa a kawo karshen wannan al’amari. “A makon jiya na lura da shigowar mutane cikin wannan azure, ciki har da… Na ga hoton dana Seyi yana zaune a baya. Ba zan lamunci haka ba. Zan bayyana muku irin mutanen da ya kamata a rika ganinsu a nan,” in ji shi.
Shugaba Tinubu ya bayyana sunayen mashawartansa; Kan Tsara Ayyuka, Hadiza Usman da na Labarai da Tsara dabaru; Bayo Onanuga da Babban Sakatarensa, Hakeem MuriOkunola da Sakatarensa Damilotun Aderemi.
“Wadannan su ne mutanen da aka yarje musu su kasance idan muna gudanar da taro kan abin da ya shafi kasa. In ban gayyace ka ba, kada ka zo, na fadi haka balo-balo. Sakataren Gwamnati da Shugaban Ma’aikata ku kula,” in ji shi.
Sai dai duk da haka ana ganin wulkawar Seyi Tinubu a wasu muhimman al’amurra kuma ana zargin akwai sa hannunsa wajen nadenaden mataimaka da mashawartan da aka aiwatar.
Dele Alake
Dele Alake, dan jarida kuma mai rajin kare hakkin dan Adam shi ne Ministan Bunkasa Ma’adinai a yanzu.
Ya taba yin aiki a karkashin Tinubu a matsayin Kwamishinan Yada Labari da Tsare-Tsare a Jihar Legas daga 1999 zuwa 2007.
An fara nada shi ne a matsayin Mai Bayar da Shawara ta Musamman kan Ayyuka na Musamman da Harkokin Sadarwa, kafin daga baya a ba shi mukamin minista.
Tsohon dan gaban goshin Tinubu ne da yake ji da shi.
Tinubu ya tabbatar da haka a sakon kewayowar ranar haihuwarsa a Oktoban da ya gabata, inda ya ce, “Alake yana da hangen nesa da kyawawan halaye da suke yin tasiri ga duk wanda suka yi hulda, yana da cikakkiyar biyayya da amana da girmamawa da kuma kyautatawa. A duk tsawon huldarmu Dele ya nuna amini ne kuma dan uwa nagari,” in ji Tinubu.
’Yan Nijeriya da dama sun zaci zai zauna a Fadar Shugaban Kasa ne a matsayin Kakakinsa sai kawai aka ga an nada shi minista.
Sai dai duk da haka ana yi masa kallon daya daga cikin wadanda suke dama furar da ake sha a gwamnatin Tinubu.
Bayo Onanuga
Onanuga wanda shi ma dan jarida ne shi ne Mai Bada Shawara ta Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da TsareTsare.
Ya rike mukamin Daraktan Gudanarwa na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) kuma shi ne Kakakin Tinubu a lokacin yakin neman zabe.
Shi ne ake kallo kamar ‘Karen Tsokana’ a gwamnatin Tinubu kasancewar yadda nan da nan yake haifar wa ’yan adawa sabon batun da za su shiga tattaunawa a kai.