’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano
Sun yi matar karaya a hannu da kafa tare da yi ma mijinta dukan kawo wuka
An gurfanar da wasu mutum uku ’yan uwan juna kan yi wa wata matar aure da mijinta dukan kawo wuƙa a yankin Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano.
An gurfanar da su ne a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Gazawa kan zargin yi wa matar auren karaya uku a ƙafarta da hannunta bayan sun yi mata dukan kawo wuƙa tare da ji mata raunuka.
Sun kuma ƙuƙƙuje mijinta da ya yi ƙoƙarin ceton ta bayan shi ma suka lakaɗa masa duka.
Ana tuhumar su laifin yin kutse da yin barazana da haɗa kai wajen aikata laifi da ji wa mutane munanan raunuka.
- ’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba
- Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku fyaɗe
Duk waɗanda ake zargin sun amsa laifukan da ake tuhumar su da aikatawa.