’Yan giya uku

Wasu mutane ne su uku suka sha giya suka yi tatil, sun fito daga gidan giyar sai suka tsayar da dan tasi; suka ce ya kai su unguwarsu. Da ya fahimci cewa a buge suke, bayan sun shiga sai ya taka totur da karfi, ya ba motar wuta, bai matsa ko’ina ba, sai ya sauko […]

’Yan giya uku
’Yan giya uku

Wasu mutane ne su uku suka sha giya suka yi tatil, sun fito daga gidan giyar sai suka tsayar da dan tasi; suka ce ya kai su unguwarsu. Da ya fahimci cewa a buge suke, bayan sun shiga sai ya taka totur da karfi, ya ba motar wuta, bai matsa ko’ina ba, sai ya sauko ya bude motar, ya ce musu: “Ku sauko, mun zo inda za ku sauka.” Na farko ya fito sai ya biya kudin motarsu duka. Na biyu ya yi godiya, shi kuma na uku sai ya falla wa dan tasi mari. Direba ya tambayi dalilin mari sai ya ce masa: “Ka yi tukin ganganci, ka kusa kashe mu, shi ya sa na mare ka!”
Daga Zee Man Fagge, Kano 08034412272

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya