’Yan gudun hijira 300 sun nutse a tekun Italiya

Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya ta ce ’yan gudun hijira 300 ne suka nutse a lokacin da suke yunkurin shiga kasar Italiya cikin wadansu kananan&nbsp jiragen ruwa ta kogin Bahar Rum a ’yan kwanakin nan.Mai magana da yawun Hukumar Carlotta Sami ta bayyana haka ne bayan ta gana da wasu […]

’Yan gudun hijira 300 sun nutse a tekun Italiya
’Yan gudun hijira 300 sun nutse a tekun Italiya

Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya ta ce ’yan gudun hijira 300 ne suka nutse a lokacin da suke yunkurin shiga kasar Italiya cikin wadansu kananan&nbsp jiragen ruwa ta kogin Bahar Rum a ’yan kwanakin nan.
Mai magana da yawun Hukumar Carlotta Sami ta bayyana haka ne bayan ta gana da wasu da mutum tara bayan jami’an kula da tekun Italiya sun tsamo su shekaranjiya Laraba.
’Yan gudun hijirar da suka tsira sun ce da dama daga cikinsu sun hallaka bayan igiyar ruwa ta yi awon gaba da su lokacin da suka shiga jiragen ruwa daga kasar Libya.
Daraktan hukumar a Turai bincent Cochetel ya ce wannan al’amari abin bakin ciki ne da za a magance faruwarsa nan gaba.
A watan Nuwamba ne kasar Italiya ta kammala aikin ceto ’yan gudun hijirar da ta kwashe shekara guda tana yi.
Sai dai hukumar ’yan gudun hijirar ta yi gargadin cewa matakin zai sanya a samu karuwar ’yan gudun hijirar da ke mutuwa.