‘Yan gudun hijira 33, 000 sun gudu Kamaru

Akallla ’yan Najeriya mutum 33,000 wadanda rikicin Boko Haram ya tilasta wa kaurace wa mullansu a yankin karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Barno ne suke gudun hijira a Jamhuriyar Kamaru. Shugaban darikar Pentecostal Fellowship reshen Jihar Barno, Bishop Mohammed Naga ne ya bayyana hakan lokacin da Gwamnan Jihar Kashim Shettima ya kai wa ’yan […]

‘Yan gudun hijira 33, 000 sun gudu Kamaru
‘Yan gudun hijira 33, 000 sun gudu Kamaru

Akallla ’yan Najeriya mutum 33,000 wadanda rikicin Boko Haram ya tilasta wa kaurace wa mullansu a yankin karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Barno ne suke gudun hijira a Jamhuriyar Kamaru.

Shugaban darikar Pentecostal Fellowship reshen Jihar Barno, Bishop Mohammed Naga ne ya bayyana hakan lokacin da Gwamnan Jihar Kashim Shettima ya kai wa ’yan gudun hijirar da ke neman mafaka a cocinsa da ke garin Maiduguri, ranar Lahadin da ta gabata.
Bishop din ya ce: “Akwai mutanen da suka kai kimanin 33,000 wadanda suka fito daga karamar Hukumar Gwoza da a yanzu suke neman mafaka a kauyuka daban-daban da ke cikin Jamhuriyar Kamaru.”
Daga bisani kuma ya bukaci gwamnatin jihar da ta kwashe su domin dawo da su Najeriya. Ya kuma ce gwamnatuin Kamaru ta ce ba za ta iya ci gaba da bai wa ’yan gudun hijira fiye da kima mafaka ba a cikin kasarta. Bishop din ya kuma shaida wa gwamnan jihar cewa akwai kimanin mutum 4,761 daga Gwoza da suke tsugunne a cocinsa, sai kuma ya bukaci kwashe su zuwa sansanonin ’yan gudun hijira.
A nasa bangaren Gwamna Shettima ya bayyana taimakon Naira miliyan 10 ga ’yan gudun hijiran a madadin gwamnatin jihar da kuma Naira miliyan daya nasa taimakon. Hakazalika, ya ba da taimakon Naira miliyan biyu domin aikin dawo da ’yan gudun hijiran da ke Kamaru zuwa Najeriya.