‘Yan gudun hijira 57,000 ne a Najeriya daga Kamaru —MDD

Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNCHR) ta ce akwai ‘yan gudun hijira 57,000 da ke zaune a jihohi uku na Najeriya. Shugaban Ofishin Hukumar da ke Kalaba, Jihar Kuros ribas, Christopher Mubanga ne ya bayyana haka a wajen bukin zagayowar Ranar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya. Ya ce, “Najeriya a yau ta […]

‘Yan gudun hijira 57,000 ne a Najeriya daga Kamaru —MDD

Wasu ‘yan gudun hijira

Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNCHR) ta ce akwai ‘yan gudun hijira 57,000 da ke zaune a jihohi uku na Najeriya.

Shugaban Ofishin Hukumar da ke Kalaba, Jihar Kuros ribas, Christopher Mubanga ne ya bayyana haka a wajen bukin zagayowar Ranar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya.

Ya ce, “Najeriya a yau ta karbi bakoncin fiye da ‘yan gudun hijirar Kamaru 57,000 a jihohin Binuwai da Kuros Riba da Taraba.

“Kuros Riba kadai na dauke da fiye da ‘yan gudun hijirar Kamaru 36,000, wato sama da kashi 63 na daukacin ‘yan gudun hijirar da ake dasu a Najeriya.”

Ya kara da cewar, a hasashen hukumar, akwai ‘yan gudun hijira miliyan 70.8, wadanda mutane ne da aka raba su da muhallansu sakamakon tarzoma a kasashensu. Haka kuma an yi hasashen mutum daya a cikin kowace dari a duniya sun kaura daga gidanjensu.

Mubanga ya alakanta bukin na UNHCR da wata kafa ce da ake amfani da ita wajen gode wa garuruwan da suka karbi bakoncinsu da ita kanta Gwamnatin Tarayya bisa taimakon da suke yi wa ‘yan gudun hijirar Kamarun.

Ya kara da cewar yanayin da aka shiga na cutar coronavirus da zanga-zangar wariyar launin fata ka iya zama silar da za a samu hadin kan duniya ta yadda kowa, har ma da ‘yan gudun hijira za su bayar da gudumuwarsu.

Majalisar Dinkin Duniya ta kirkiri ranar ne domin jijina wa karfin hali da juriyar mutanen da yaki ko zalunci ya tilasta musu barin gidajensu.