’Yan gudun hijira da suka koma yankunansu sun koka da rashin asibitoci

Duk da kokarin da Gwamnatin Jihar Borno ke cewa tana yi na fara aikin sake gina garuruwan da yakin Boko Haram ya daidaita don sake tsugunar da ’yan gudun hijira a garuruwa, har yanzu mutanen da suke zaune a wadannan wuraren ba su daina fuskantar kunci ba saboda rashin asibitoci da maguguna sanadiyyar rushewa ko […]

’Yan gudun hijira da suka koma yankunansu sun koka da rashin asibitoci
’Yan gudun hijira da suka koma yankunansu sun koka da rashin asibitoci

Duk da kokarin da Gwamnatin Jihar Borno ke cewa tana yi na fara aikin sake gina garuruwan da yakin Boko Haram ya daidaita don sake tsugunar da ’yan gudun hijira a garuruwa, har yanzu mutanen da suke zaune a wadannan wuraren ba su daina fuskantar kunci ba saboda rashin asibitoci da maguguna sanadiyyar rushewa ko kuma kone wadanda ake da su da ’yan Boko Haram suka yi a shekarun baya.
Malam Hassan Usman, dan gudun hijira ne daga garin Baga. Ya ce suna fama da rashin ginannun asibitoci da magunguna saboda rusa asibitocin da Boko Haram suka yi, kuma jama’a da dama na ta mutuwa, musamman mata masu juna biyu, inda za ka ga mace tana nakuda amma babu yadda za ta yi. “Kafin wani lokaci za ka ga gawarta ko ta jariri, a wani lokacin kuma za ka ga marasa lafiya suna gargarar mutuwa amma babu yadda mutum zai yi saboda rashin asibitoci da likitoci ko  magunguna. Wallahi wannan abu yana bata mana rai, domin a kan haka ne ma akasarinmu muka bar Baga zuwa nan Maiduguri. Don haka muke rokon gwamnati ta gina asibiti a garin Baga kuma ta samar da magunguna da likitoci, domin ceto rayukan al’umma.”
Ita ma Malama Falmata da ta fito daga karamar Hukumar Dikwa, ta ce: “Wallahi a garin Dikwa babu wani asibitin da muke zuwa don haihuwa ko don rashin lafiya, domin duk Boko Haram sun kone akasarin kananan asibitocinmu da dakunan shan magani da kemis-kemis kuma sun yi awon gaba da sauran magunguna. Idan mutum yana da mace mai  juna biyu ko marar lafiya, to ya shiga fargaba ke nan, ba shi da kwanciyar hankali, sai dai ya dauko marar lafiyar zuwa Maiduguri, kuma ta iya yiwuwa kafin mutum ya kawo Maiduguri rai ya yi halinsa. To ka ga wannan abin ya ishe mu, don haka muna roko ku gaya wa gwamnati ta gina asibitoci da samar da magunguna domin amfanin mu mutanen karkara, da muke cikin wahala.”
kungiyar Manyan Likitoci ta Jihar Borno, ta tabbatar tare da kokawa kan rashin isassun asibitoci da likitoci a akasarin kananan hukumomin da ’yan Boko Haram suka daidaita, inda ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka wajen gina asibitocin.
A cewar Dokta Yakubu Nyadayiti, babban likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri: “A gaskiya ana karancin asibitoci a yankunan kananan hukumomin da yakin Boko Haram ya daidaita, domin kuwa akasarin al’ummomin da ke zaune a wuraren suna ketarowa ne nan garin Maiduguri don samun magunguna. Kuma ga shi akasarin asibitocin Maidugurin sun cike da majinyata, musamman wadanda suka fito daga kauyuka ko kananan hukumomin da Boko Haram suka kwace, a can kuma akwai mutane da dama da suka koma, to amma ba su da likitoci balle asibitoci da magunguna. Don haka muna rokon gwamnati da ta taimaka wajen samar da asibitoci da likitoci da magunguna ga mutanen yankunan don guje wa cinkoso a asibitocin garin Maiduguri.”
A nata bangaren, Gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar wa jama’ar jihar, musamman ’yan gudun hijira cewa za ta yi iya kokarinta wajen sake gina yankunan da yakin Boko Haram ya daidaita kuma su koma yankunan nasu nan ba da dadewa ba, kamar yadda Gwamnan Jihar, Alhaji Kashim Shettima ya fada a lokacin da ya kai ziyarar gani aikin sake gina garuruwan.