’Yan gudun hijira dubu 25 sun koma gidajensu a Zamfara
Akalla ‘yan gudun hijira dubu 25 da suka bar gidajensu saboda matsalar ‘yan bindiga a kauyuka da biranen Zamfara yanzu sun koma gidajensu sakamakon zaman lafiya da aka samu sanadiyyar kokarin Gwamnan jihar Bello Matawalle. Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Zamfara (ZEMA) Alhaji Sanusi Kwatarkwashi, ne ya sanar da hakan a tattaunawar da […]
Akalla ‘yan gudun hijira dubu 25 da suka bar gidajensu saboda matsalar ‘yan bindiga a kauyuka da biranen Zamfara yanzu sun koma gidajensu sakamakon zaman lafiya da aka samu sanadiyyar kokarin Gwamnan jihar Bello Matawalle.
Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Zamfara (ZEMA) Alhaji Sanusi Kwatarkwashi, ne ya sanar da hakan a tattaunawar da ya yi da Wakilin kamfanin dillancin labarai NAN yau a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Alhaji Sanusi, ya kara da cewa sun taba samun adadin ‘yan gudun hijira da suka kai dubu 37 saboda tsananin hareharen ‘yan bindigar jihar. A yanzu bayan komawar jama’ar gidan sun ci gaba da rayuwar su, kamar kasuwanci, noma da kiwo da sauran sana’o’i.