’Yan gudun hijira na bukatar tallafi – Shugaban kungiyar Muryar Talaka
Shugaban kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Yobe Malam Saleh Bakwaro ya roki gwamnatin jihar da ta kawo daukin gaggawa ga ‘yan gudin hijirar yankunan kananan hukumomin Gujba da Gulani da akasarinsu ke cikin garin Damaturu fadar jihar sanadiyyar karbe yankunansu da ‘yan bindiga suka yi. Shugaban kungiyar muryar talakan ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa […]
Shugaban kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Yobe Malam Saleh Bakwaro ya roki gwamnatin jihar da ta kawo daukin gaggawa ga ‘yan gudin hijirar yankunan kananan hukumomin Gujba da Gulani da akasarinsu ke cikin garin Damaturu fadar jihar sanadiyyar karbe yankunansu da ‘yan bindiga suka yi.
Shugaban kungiyar muryar talakan ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Aminiya a garin Damaturu dangane da halin da wadannan ‘yan gudin hijira ke ciki kan matsalolin rayuwa da suke fuskanta.
Ya ci gaba da cewa wadannan ‘yan gudin hijira da suka fito daga yankunan Gujba da Gulani na da matukar yawa maza da mata da aksarinsu saboda tsananin halin matsin da suke ciki musamman ta bangaren rashin ishasshen muhalli da rashin abinci da sana’ar yi kasancewar aksarinsu manoma ne da suka dogara da aikin gona don samun abin masarufi za ka gan su a warwatsen cikin gari ba sana’ar yi, sai dai ka gansu su da iyalensu su na bin titi-titi kwararo-kwararo da tashoshin mota suna bara.
Malam Saleh Bakwaro ya kara da cewa wannan hali da wadannan ‘yan gudin hijira ke ciki suna bukatar taimakon daga gwamnatin jihar. Agajin da wasu
daidaikun kungiyoyi ke bayar wa bai isa ba domin kuwa suna bukatar ninka kokarin da ake yi. Hasali ma akwai bukatar gaggawa na a samar mu su da karin
sansanin da za a ajiye su musamman ganin cewar damina ta fara sauka ta yadda za su bukaci muhalli mai nagarta.