’Yan gudun hijira na cin shinkafa tirela uku kullum a Borno – Shettima
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya ce kimanin buhun shinkafa 1,800 wato tirela uku ’yan gudun hijirar da suke sassan jihar suke cinyewa a kullum.Gwamna Kashim Shettima ya bayyana haka ne a wajen taro na farko wanda za a rika yi duk shekara kan sake gina Jihar Borno wadda rikicin Boko Haram ya daidaita.Wata […]
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya ce kimanin buhun shinkafa 1,800 wato tirela uku ’yan gudun hijirar da suke sassan jihar suke cinyewa a kullum.
Gwamna Kashim Shettima ya bayyana haka ne a wajen taro na farko wanda za a rika yi duk shekara kan sake gina Jihar Borno wadda rikicin Boko Haram ya daidaita.
Wata kungiyar agaji ta mai suna AOA Global da Gidauniyar Rhodes Trust da kuma gwamnatin Jihar ta Borno ne suka dauki nauyin za su rika shirya taron, wanda aka fara karo na farko a Abuja, a ranar Talatar da ta gabata.
Gwamna Shettima wanda ya dauki dogon lokaci yana bayani kan bukatar abinci da ake da ita sakamakon karuwar ’yan gudun hijirar da mayakan Boko Haram suka rutsa da su kafin sojoji su ceto su, ya ce: “A yanzu da muke magana muna fama da matsalar ciyar da dimbin mutane a Jihar Borno. Sojoji sun samu nasarar ceto mutanen da ’yan Boko Haram suka rutsa da su sakamakon kawanyar da suka yi musu. daruruwan wadanda aka ceto suna kwarara zuwa sansanonin ’yan gudun hijira daga yankunan da aka kwato. A yau a Jihar Borno kimanin buhunan shinkafa masu girman kilo 50 guda 1,800 wato tirela uku masu daukar buhu 600 kowacce ake bukata a kullum domin ciyar da ’yan gudun hijirar da suke sassan jihar, kuma wannan bai hada da kayan miya da suka hada da tumatur da manja ko man gyada da wake da albasa da gishiri da sauransu ba.”
Gwamna Shettima ya ce ’yan gudun hijirar da ke sansanonin Ngala da suka kai 7,000 da kuma dubu 60 da ke zaune a cikin garin ba su da abinci sosai domin kuwa a kullum ana dafa musu shinkafa buhu 140.
Ya lissafo yadda ake dafa shikafar a sansanonin da suka hada da buhu 978 a Maiduguri da Jere da Dikwa da Bama da kuma Damboa. Sai Monguno da Marte buhu 60 a kullum sai Baga da Kiroskawa buhu 58, Sabon Gari buhu 40.
Ya yaba wa kungiyoyin Red Cross da Red Crescent da gwamnatocin Amurka da na Ingila da na Norway da hukumomin Majalisar dinkin Duniya da suka hada ta abinci da UNICEF da sauran kungiyoyin agaji kan tallafa wa jihar da suke yi.
which has been of unimaginable humanitarian support to Borno, conbeyed 33 trucks, each carrying 600 Ya ce kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta ce a ba jihar buhunan shinkafa dubu 21 da man girki da suturun da Hukumar Kwastam ta kwace daga masu fasakwauri kuma suna kokarin dauko su daga Legas zuwa Maiduguri don ciyar da ’yan gudun hijirar.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Lafiya Farfesa Isaac Folorunso Adewole da na Masana’antu Dokta Kayode Fayemi da Babban Jami’in kididdiga na kasa Dokta Yemi Kale, da daraktocin hukumomin bunkasa kasashe na Ingila da Amurka da sauransu.