‘Yan gudun hijira na fama da sarar macizai

‘Yan gudun hijira dake sansaninsu a Gongola dake birnin tarayya Abuja sun bukaci hukumomi da su tallafa masu wajen samar masu ruwan sha da wuraren ba-haya. ‘Yan gudun hijirar sun ce a duk lokacin da suka je neman ruwa macizai na sarar su. Sun bayyana korafin nasu lokacin da ayarin kuniyar tsaftar muhalli ta Najeriya […]

‘Yan gudun hijira na fama da sarar macizai
‘Yan gudun hijira na fama da sarar macizai

‘Yan gudun hijira dake sansaninsu a Gongola dake birnin tarayya Abuja sun bukaci hukumomi da su tallafa masu wajen samar masu ruwan sha da wuraren ba-haya.

‘Yan gudun hijirar sun ce a duk lokacin da suka je neman ruwa macizai na sarar su.

Sun bayyana korafin nasu lokacin da ayarin kuniyar tsaftar muhalli ta Najeriya da wasu kungiyoyi masu zaman kansu irin su: kungiyar ‘WaterAid’ da ‘Action Against Hunger’, suka ziyarci sansanin.

Shugaban sansanin ‘yan gudun hijirar Mista Joseph Jauro ya bukaci a masu fada aji da su bayar da agajin gaggawa don kaucewa kamuwa da cututtuka irinsu amai da gudawa sanadiyyar shan gurbataccen ruwa.