‘Yan gudun hijira sun koka kan halin da suke ciki a Nasarawa

’Yan gudun hijirar da suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira da suke garuruwan Kadarko da Agyaragu a karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa sun yi kira ga gwamnatin jihar ta cika alkawarin tallafin Naira miliyan bakwai da ta yi musu kwanakin baya.  ’Yan gudun hijirar wadanda galibinsu wadanda rikicin manoma da makiyaya a jihar […]

‘Yan gudun hijira sun koka kan halin da suke ciki a Nasarawa

’Yan gudun hijirar da suke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira da suke garuruwan Kadarko da Agyaragu a karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa sun yi kira ga gwamnatin jihar ta cika alkawarin tallafin Naira miliyan bakwai da ta yi musu kwanakin baya. 

’Yan gudun hijirar wadanda galibinsu wadanda rikicin manoma da makiyaya a jihar ya shafa ne, mai magana da yawunsu, Mista bictor Gwer ya bayyana wa wakilinmu cewa a halin yanzu suna fuskantar matsalolin rayuwa da dama tun bayan da aka rabo su da gidajensu suka zo sansanin. 

To amma ya gode wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura dangane da tallafin  kayayyakin agaji da gwamnatinsa ta ba su kwanakin baya, inda ya bukaci ya cika alkawarin Naira miliyan bakwai da ya yi musu don a cewarsa kudin zai taimaka musu sosai wajen rage musu wahalhalun da suke fuskanta a sansanin. 

Ya ce “Ka ga wadannan kayayyakin agaji da Gwamnan ya turo aka raba mana kwanakin baya sun kare. Shi ya sa ma da aka raba kayayyakin abinci wadansu ma katon din Indomie biyu kacal suka samu kowannensu don muna da yawa. Mutanenmu a nan suna cikin tsananin wahala kuma ba za mu iya komawa gidajenmu ba domin wadannan Fulani makasa sun koma zama a kauyukanmu ga kuma kayayyakin gonakinmu sun zama abincin dabbobinsu.” 

Wadansu daga cikinsu wadanda suka gana da wakilinmu da suka bukaci a sakaya sunayensu sun yi kira ga Gwamna Al-Makura ya yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa duk lokaci da zai cika alkawarin ya bi ta hanyar da ta dace zuwa gare su don tabbatar da adalci a yayin rabon. 

Haka ’yan gudun hijirar da ke garin Kadarko sun bayyana takaicinsu dangane da yadda a cewarsu galibinsu ba sa amfana da rabon kayayyakin agaji da gwamnati da sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni ke ba su, inda suka ce sau da yawa wadanda ba ’yan gudun hijira ba ne ke amfana da kayayyakin maimakon asalin ’yan gudun hijirar da aka ba su kayayyakin. 

A kwanakin baya ne Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya bai wa masu gudun hijirar tallafin kayayyakin agaji a madadin gwamnatinsa, inda daga bisani ya yi  alkawarin ba su tallafin Naira miliyan 7 don rage musu wahala.