‘Yan gudun hijira suna cikin yunwa – MDD
Ana bukatar akalla tan dubu 30 na abinci don ciyar dubbban ’yan gudun hijiran rikicin Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabas, kamar yadda wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Mohamed Safieldin ya bayyana. Ya ce kayan agajin da ake da su yanzu sun yi karanci. “Ko wanda yake zuwa daga hannun gwamnatin, ko daga kasashen ketare, […]

Ana bukatar akalla tan dubu 30 na abinci don ciyar dubbban ’yan gudun hijiran rikicin Boko Haram a yankin Arewa-maso-Gabas, kamar yadda wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Mohamed Safieldin ya bayyana.
Ya ce kayan agajin da ake da su yanzu sun yi karanci. “Ko wanda yake zuwa daga hannun gwamnatin, ko daga kasashen ketare, ba ya wadata,” kamar yadda ya bayyana.
“Dimbin mutane ba sa iya cin abinci sau biyu a rana, muna maganar mutane fiye da miliyan daya ne. Akwai aqalla mutane dubu 800 daga cikinsu da suke bukatar taimakon abinci” inji shi.