’Yan gudun hijirar Afghanistan 531 sun koma gida daga Pakistan
A ranar 15 ga watan Agustan 2021 ne Taliban ta kwace iko da Afghanistan.
Ma’aikatar ’Yan Gudun Hijira ta Afghanistan, ta ce ’yan gudun hijira 531 ne suka dawo gida daga Pakistan a cikin kwanaki biyun da suka gabata.
Fiye da ’yan gudun hijirar Afghanistan miliyan 2.5 da aka yi wa rajista ne ke zaune a Pakistan da Iran.
- Ta watsa wa budurwar mijinta ruwan zafi a fuska
- Abin da muka tattauna da Tinubu kan rikicin Mali —Jonathan
Makwanni biyu da suka gabata, kamfanin dillancin labarai na Bakhtar ya bayyana cewar ’yan gudun hijirar Afghanistan fiye da ne 60,000 suka dawo gida daga Iran tun a watan Janairu.
Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Afganistan ta bukaci ’yan gudun hijirar kasar da ke kasashen waje da su koma gida su bayar da tasu gudunmuwar wajen sake gina kasarsu da yaki ya daidaita.
A ranar 15 ga Agustan 2021 ce kungiyar Taliban ta kwace mulkin Afghanistan, bayan sojojin Amurka sun fice daga kasar.
Sojojin kawancen Amurka sun shafe shekara 20 a Afghanistan, inda suka kifar da gwamnatin Taliban da ta shekara shida tana jagorantar kasar daga 1996 zuwa 2001.
Duk da ikirarin Taliban na kawo karshen danniya, amma alamu su nuna tsugune ba ta kare ba.
A watan Satumban 2022, kungiyar ta kaddamar da sabuwar gwamnatin wucin gadi, wadda a ciki ta bai wa masu tsattsauran ra’ayi muhimman mukamai ba tare da bai wa mata wata dama ba.
Kungiyar ta dawo da Ma’aikatar Inganta Kyawawan Dabi’u da Hana Aikata Laifuka, wadda aka dakatar.
Wannan mataki ya haifar da zanga-zanga a birnin Kabul da Herat.
Bayan an sake bude makarantu a watan Maris din 2022, hukumomin Taliban suka kafa tsauraran dokoki da suka hada da haramta wa ’yan mata zuwa makarantun sakandare.
Sun kuma wajabta wa ma’aikatan gwamnatin kasar ajiye gemu.