’Yan gudun hijirar Baga dubu uku sun isa Maiduguri
Jama’a da dama da suka yiwo gudun hijira daga Baga zuwa Maiduguri da suka haura dubu uku, sun isa Maiduguri inda aka sauke su a sabon sansanin da aka yi musu a rukunin gidaje na Dokta Shettima Ali Monguno. daya daga cikin ’yan gudun hijirar Malam Bala Baga, mai sana’ar kamun kifi a Tafkin Chadi, […]
Jama’a da dama da suka yiwo gudun hijira daga Baga zuwa Maiduguri da suka haura dubu uku, sun isa Maiduguri inda aka sauke su a sabon sansanin da aka yi musu a rukunin gidaje na Dokta Shettima Ali Monguno.
daya daga cikin ’yan gudun hijirar Malam Bala Baga, mai sana’ar kamun kifi a Tafkin Chadi, ya shaida wa wakilinmu cewa, “A gaskiya da kyar muka tsira daga harin da ’yan Boko Haram suka kawo Baga, domin sun fara kai hari ne ga barikin soja, kuma sojojin sun gudu, kwatsam sai suka nufo kanmu, wasu suka tsira ta ruwa zuwa kasar Nijar da Chadi, mu kuma muka nufo Maiduguri. Gaskiya mun ga dimbin gawarwakin mutanen Baga, sun kashe mutane da yawa kuma sun kone garin da kewayensa.”
Ya ce su da mata da yara da suka yiwo Maiduguri sun samu tallafin gwamnatin Jihar Borno wadda ta aika musu da manyan safa-safa sama da 30 a inda suka yada zango su sama da dubu uku aka kwaso su aka kawo su Maiduguri.
Ya ce a yanzu suna cikin zullumin ko an kashe sauran ’yan uwansu da matansu da ’ya’yansu da kowa ya yi ta kansa.
Wata ma suna Malama Fatuma daga cikin ’yan gudun hijirar ta ce ba ta san inda ’ya’yanta uku suke ba, saboda sun fita da Asuba zuwa kasuwar Kifi kuma har yanzu ba ta san inda suke ba.