”Yan gudun hijirar Bama sun fara komawa gida

Sakamakon bude hanyar Maiduguri zuwa Bama da amincewar da hukumomin tsaro suka yi cewa zaman lafiya ya dawo a garin Bama wanda ya shafe shekara hudu ba mutane a cikinsa saboda hare-haren Boko Haram, yanzu haka gwamnatin Jihar Borno ta fara mai da mutanen Bama gida daga gudun hijira da suke yi Maiduguri. A jawabin […]

”Yan gudun hijirar Bama sun fara komawa gida

Sakamakon bude hanyar Maiduguri zuwa Bama da amincewar da hukumomin tsaro suka yi cewa zaman lafiya ya dawo a garin Bama wanda ya shafe shekara hudu ba mutane a cikinsa saboda hare-haren Boko Haram, yanzu haka gwamnatin Jihar Borno ta fara mai da mutanen Bama gida daga gudun hijira da suke yi Maiduguri.

A jawabin Gwamnan Jihar Alhaji Kashim Shettima ga ayarin farko masu komawar ya ce “Za a kwashe mutanen ne daki-daki kuma sai an tantance su kafin su shiga gidajensu, kuma za a ba kowanensu buhunan abinci da kayayyakin bukatun yau da kullum, kafin su saba. Na san za su samu matsaloli musamman ta fuskar harkar tsaro, to su daure su yi hakuri kuma su bai wa jami’an tsaro cikakken hadin kai da goyon baya lokacin tantance na kwarai da na banza.”

Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Usman Jidda Shuwa a wani taron manema labarai da ya kira a ofishinsa kwana biyu bayan bude hanyar Bama, ya ce “Gwamnatin Jihar ta shirya tsaf don mai da mutanen Bama zuwa garinsu, saboda an kammala gina gidaje dubu 10 da ma’aikatun gwamnati da babbar kasuwar garin da wuraren ibada, kuma an samar da kayayyakin bukatun yau da kullum da suka hada da hanyoyi da ruwan sha da asibitoci da makarantu, inda ake sa ran sama da mutum dubu 10 za su iya komawa garin ba tare da wata matsala ba.”

Ya ce an tsara jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda da na shigi-da-fici da na yaki da miyagun kwayoyi da sibil difens da na farin kaya za su kasance a garin.

Ya ce an samar da motocin da za su kai su bisa tsarin kowace unguwa ko kauye ko gari da ranar da za a dauke su, kuma kowane mutum an tsara yadda za a gane gidansa, don haka ya nemi hadin kai da goyon bayan mutanen don samun nasarar komawa garinsu.

Zuwa hada wannan rahoto an yi biyu, wajen mayar da ’yan gudun hijirar ana kai kowa gidansa tare da iyalansa ba tare da wata matsala ba.

Malam Modu Kachallah,wani dan asalin Bama ya shaida wa wakilinmu cewa “A gaskiya gwamnatin Borno da jami’an tsaro sun taimaka mana sosai wajen dawowarmu garinmu, an gyara mana gidajenmu, an dauko mu an kawo mu, sannan an ba mu abinci da kayayyakin bukatun yau da kullum, ga jami’an tsaro suna gudanar da ayyukansu a garin. Mun gode Allah kuma mun gode wa gwamnatin Borno da jami’an tsaro domin yanzu rayuwarmu za ta koma kamar da, muna fata babu wani abin da zai sake faruwa.”

Kwamishinan Ma’aikatar Ginawa da Gyarawa da Tsugunar da ’Yan Gudun Hijira, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce duk gidan da ba a gyara ba za a bai wa mai gidan wasu ’yan kudi don ya gyara, saboda an gina tare da gyara gidaje sama da dubu 10 ne ba duka ba, sai babbar kasuwa da asibiti da ofishin ’yan sanda da Sakatariyar Karamar Hukuma da gwamnatin jihar ta yi tare da taimako daga hukumomin UNHRC da PCNI da bSF.

Komawa Bama ta zama zakaran gwajin dafin tsarin mai da mutane gida da suka hada da garuruwan Gwoza da Mobar da Dikwa da Gamboru Ngala da gwamnatin jihar ta sha alwashin aiwatarwa kafin ranar 29 ga Mayun bana, in jami’an tsaro suka bayar da tabbacin dorewar zaman lafiya a garuruwan.