’Yan gudun hijirar Damboa sun watse saboda kwalara
Mutanen Damboa da ke gudun hijira a garin Biu bayar da mayakan Boko Haram suka tarwatsa garinsu sun fara kaurace wa sansanoninsu saboda bayyanar cutar kwalara a sansanonin.Mutanen Damboa da ke gudun hijira a Biu sun kai dubu 14, to amma yanzu bayanai sun ce akasarinsu sun bar sansanonin zuwa wasu wurare daban bayan da […]
Mutanen Damboa da ke gudun hijira a garin Biu bayar da mayakan Boko Haram suka tarwatsa garinsu sun fara kaurace wa sansanoninsu saboda bayyanar cutar kwalara a sansanonin.
Mutanen Damboa da ke gudun hijira a Biu sun kai dubu 14, to amma yanzu bayanai sun ce akasarinsu sun bar sansanonin zuwa wasu wurare daban bayan da aka ruwaito kwalara ta kashe sama da yara 20.
Jami’in Hukumar NEMA a shiyyar Arewa maso Gabas, Muhammad Kanar ya tabbatar wa manema labarai a Maiduguri cewa “Gaskiya ce an samu barkewar cutar kwalara a sansanonin na, sai dai ya ce yara 9 ne kwalara ta kashe, sannan mutum 24 sun rasu har da wadanda maleriya ta halaka su, kuma abin ya yi sauki.
Ya ce su da likitocin sa-kai (Doctors without Borders) da ’yan agajin Red Cross suna raba magunguna da kayayyakin bukatun yau da kullum da kokarin dakile cututtukan biyu, musamman maleriya da ta halaka mutum 14.
Muhammad Kanar ya ce akwai ’yan gudun hijira dubu 44 a Jihar Adamawa, sai Borno
dubu 183, sai kuma Jihar Yobe sama da dubu 30, “domin mun samu labarin mutanen Gujuba da Buni-Yadi da Buni-Gari duk sun tare a Damaturu, kuma muna kokarin mu ga cewa mun agza masu da kayayyakin abinci da magunguna da sauransu.