’Yan gudun hijirar Kamaru a Kuros Riba
Mutanen karamar Hukumar Boki a Jihar Kuros Riba suna fuskantar matsala sakamakon kwararowar mutanen Kamaru fiye da dubu 8, da suke gudun hijira daga yankin yammacin kasar mai amfani da harshen Ingilishi [Anglophone]. Sama da ’yan gudun hijira dubu 15 ne, aka ce sun mamaye kauyukan da dama na Kuros Riba kuma a cewar kiyasin […]
Mutanen karamar Hukumar Boki a Jihar Kuros Riba suna fuskantar matsala sakamakon kwararowar mutanen Kamaru fiye da dubu 8, da suke gudun hijira daga yankin yammacin kasar mai amfani da harshen Ingilishi [Anglophone]. Sama da ’yan gudun hijira dubu 15 ne, aka ce sun mamaye kauyukan da dama na Kuros Riba kuma a cewar kiyasin Majalisar dinkin Duniya, adadin masu gudun hijirar a jihar yana iya kaiwa sama da mutum dubu 30. Rahotanni sun ce kimanin ’yan gudun hijira dubu 6 sun isa kauyukan a mako biyu da suka wuce, a yayin da wasu dubu biyu suka biyo baya ta satattun hanyoyin kan iyakar kasashen biyu.
Masu kaura da ke magana da harshen Boki ne da ’yan gudun hijira suna ci gaba da tururuwa zuwa yankunan ne sakamakon dimbin sojojin Kamaru da aka tura yankunansu. Da damansu sun gudu zuwa garin Bashua, wanda shi ne gari na karshe a tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Yawan masu neman mafakar ta fi karfin dan karamin garin na Bashua da wani gari da ake kira Erinekpang wadanda suka zama mafaka da masu gudu daga Kamaru suke tsugunnawa. Yawansu yana jawo wahalar abinci da na kiwon lafiya musamman ruwan sha domin mutanen galibi suna dogara ne da ruwan koramu wadanda a wasu lokuta suke kafewa.
Wannan sabuwar matsala ta ’yan gudun hijira a Afirka tana da alaka da batun neman ballewa na masu Magana da harshen Ingilishi a yankin Kudu maso Yamma na Kamaru. Har zuwa 1959 wannan yanki hade da yankin Mubi da Dutsen Mambila suna karkashin mulkin Birtaniya da Faransa ne a karkashin izinin Majalisar dinkin Duniya, a baya sun kasance a karkashin mulkin mallakar Jamus ce, inda aka karbe su bayan samun nasara a kan Jamus lokacin Yakin Duniya na daya. Yayin da Mubi da Mambila suka kada kuri’ar kasancewa a karkashin Najeriya a kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Majalisar dinkin Duniya ta shirya (suka zama Lardin Sardauna da ke jihohin Adamawa da Taraba a yanzu), Kudu maso Yammacin Kamaru ya kada kuri’ar kasancewa a Kamaru.
Idan bayan wadannan shekaru, mutanen wancan yanki a yanzu suna son ballewa daga Kamaru, wajibi ne mu shaida musu balo-balo cewa hadewa da Najeriya ba shi ne zabi ba. Suna da zabi uku a 1959: su hade da Kamaru ko su hade da Najeriya ko su kasance kasa mai ’yancin kanta. Kuma kamar yadda kowace kasa za ta so ta kara fadin kasarta a namu lamarin yunkurin ballewarsu tana iya dawo da Bakassi ga Najeriya, don haka bai kamata Najeriya ta karfafa yunkurin ballewa a yankin da ke Magana da Ingilishi na Kamaru ba. Mu ma a ’yan kwanakin baya mun yi fama da matsalar masu neman ballewa da kungiyar IPOB da ke kusa da yankin da ke Magana da Ingilishi ta jagoranta. Wajibi ne mu girmama sahihiyar yarjejeniyar OAU ta girmama iyakokin da aka gada daga Turawan mulkin mallaka, ba don komai ba, ko don kada a bude kofofin da za su jawo bala’i. Kuma duk da sabaninmu a kan Bakassi, Kamaru ta taimaka ne sosai a kan yaki da Boko Haram kuma har yanzu tana dauke da ’yan gudun hijirar Najeriya a Arewacin kasarta.
Kuma baya ga haka akwai alkawarin kasashen duniya a wuyan Najeriya na tallafa wa ’yan gudun hijira. Don haka hukumomin Tarayya irin su Hukumar Kula da ’Yan gudun Hijira ta kasa da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya da suke tallafa wa miliyoyin ’yan gudun hijira a Arewa maso Gabas, akwai bukatar a turo wannan yankin don taimaka wa ’yan gudun hijirar Kamaru. Gwamnatocin jiha da na kananan hukumomin yankin ma wajibi ne su taimaka, haka kungiyoyi masu zaman kansu da al’ummar yankin da kungiyoyin kasashen duniya. Domin a kauce wa tashin hankali da karya doka da oda, wajibi ne Najeriya ta tsaurara tsaro a kan iyakokinta tare da bai wa ’yan gudun hijirar matsuguni da taimako cikin gaggawa har zuwa lokacin da za su iya komawa garuruwansu.
Kuma ba kula da su kadai ba, wajibi ne Najeriya ta shiga a dama da ita wajen nemo hanyar magance karuwar matsalar neman ballewa daga Kamaru, wadda it ace tushen jawo gudun hijirar. Matukar ba a samu hanyar warware matsalar cikin lumana ba, matsalar za ta ci gaba da tabarbarewa kila ma ta dauki tsawon shekaru. Sabanin Boko Haram wadda ba ta amince da halaccin hukumomi ba, kuma wadda ba ta amince da sulhu ba, matsalar da ke Kamaru hakika wadda za a iya sulhunta ta ce daga shugabannin siyasa da suka san ya kamata.
Wajibi ne Shugaba Paul Biya ya nemi hanyar lumana wajen magance matsalar, kuma mu taimaka masa gwargwadon abin da za mu iya yi. A matsayinmu ta kasa da muka hadu da Yakin Basasa da na masu dauke da makamai da kuma ’yan ta’adda a shekara 40 da suka gabata, muna da hujjar da za mu shawarci makwabciyarmu Kamaru ta yi taka-tsantsan dominkada ta fada cikin irin wannan mugun hali.