’Yan gudun hijirar Najeriya 4,000 sun dawo daga Nijar

Kimanin ’yan gudun hijira ’yan Najeriya 4,000 da suka yi kaura zuwa Jamhuriyar Nijar a lokacin da ta’addancin Boko Haram ya yi kamari ne suka dawo gida Najeriya a watan da ya gabata. Wannan bayani ya fito ne daga ofishin kula da ba da agaji na Majalisar dinkin Duniya (UN-OCHA) a Arewa maso Gabas . […]

’Yan gudun hijirar Najeriya 4,000 sun dawo daga Nijar

Kimanin ’yan gudun hijira ’yan Najeriya 4,000 da suka yi kaura zuwa Jamhuriyar Nijar a lokacin da ta’addancin Boko Haram ya yi kamari ne suka dawo gida Najeriya a watan da ya gabata. Wannan bayani ya fito ne daga ofishin kula da ba da agaji na Majalisar dinkin Duniya (UN-OCHA) a Arewa maso Gabas . Kamar yadda rahoton kwamitin ya nuna, an amshi ’yan gudun hijirar ne da suka yiwo kaura a wurare daban-daban na Jihar Borno a cikin watan Oktoba da ya gabata. Takardar kididdigar ta nuna cewa ’yan gudun hijira 1,470 ne suka koma Gwoza, guda 498 suka koma Kukawa, guda 374 suka koma Ngala, sai kuma mutum 250 suka koma garin Dikwa.

A cewar Kwamitin na UN-OCHA, kungiyon jin kai sun taimaka wa ’yan gudun hijirar da suka dawo da tallafin suturu da wuraren zama. Kuma sakamakon daukewar ruwan sama, kungiyoyin agaji sun shirya yadda za su samar wa ’yan gudun hijirar da wuraren zama a Munguno ga mutum 2,560, sai Damboa, mutumm 2,075, sai Bama mutum 2000, sai Gwoza mutum 1,560, sai Kala-Balge mutum 1000, sai Mobar mutum 975, sai Dikwa mutum 680, sai Kaga mutum 540, sai Yola ta Arewa mutum 300, sai Damaturu mutum 181, sai kuma a Jere mutum 158.

Kuma domin magance matsalar wurin zama kimanin ’yan gudun hijirar dubu 688 da 314 ne aka yi wa rajista a kananan hukumomin Bama da Damboa da Konduga da Ngala a Jihar Borno da kananan hukumomin Madagali da Yola ta Kudu a Jihar Adamawa. Kuma kimanin matasa ’yan gudun hijira ’yan kasa da shekara 17 su dubu 102 da 800 za a samar musu da katin shaidar wurin haihuwa a garuruwan Damasak da Banki da Gamboru-Ngala da Monguno a Jihar Borno. Haka kuma an taimaka wa mutum dubu 20, domin su samu katin shaidar haihuwa da takardun shaidar wurin zama da ake bukatar kafin a ba su Katin Shaidar dan kasa.

Game da shirin kare mata daga cin zarafi (GBb), rahoton ya nuna an tallafa wa mata dubu 71 da 850 aka ba su kayayyakin tsabta da kiwon lafiya, yayin da aka bayar da shawarwari da tausar mata dubu 12 da 650 daga cikinsu. Kuma an horar da ma’aikatan jin kai da ’yan aikin sa kai, 1,250 kan kare matan da aka ci zarafinsu (GBb), yayin da aka horar da wadansu mazauna karkara kimanin dubu 52 da 750 dabarun da suka kamata su bi wajen kare kai daga cin zarafin da ake yi wa mata.

“Fiye da yara dubu 18 da 650 ne suka samu tallafin shawarwari, yayin da aka samu nasarar hada wadansu yara 25 da iyayensu na asali sannan yara 600 da aka ceto daga kungiyar Boko Haram, suka ci gajiyar cikakkun ayyukan kare yara,” inji ta.

Hukumar UN-OCHA ta ce Hukumomi Uku domin aikin sa kai na Dawo da ’Yan gudun Hijirar Najeriya daga Kamaru za su ci gaba da  kai ziyara ga yankunan da lamarin ya shafa a wani bangare na tsara ayyukan shekarar 2018.

Ta bayyana cewa wakilai daga kasashen Kamaru da Nijar za su ziyarci Adamawa da Yobe da Damasak domin duba yankunan da aka gano za su karbi kashi na farko na ’yan gudun hijirar da ake sa ran dawowarsu a watan Janairun badi.

Kuma za a gudanar da kamfe din wayar da kai na kwana 16 a watan Disamban bana a wani bangare na bikin Ranar Yaki da Cin Zarafin Mata ta Duniya.

Takardun sun bayyana cewa, hukumar ta Majalisar dinkin Duniya da hadin gwiwar masu bayar da tallafin jin kai za su bayar da fiffiko wajen tsara kai daukin tallafi ne bisa dogaro da dabarun shekarar 2017 da kuma bukatar shigo da bukatun daukaka ingancin muhalli da daidaiwa da kula da sansanonin ’yan gudun hijira.“Sakamakon shiga lokacin rani da kuma ci gaba da ayyukan sojoji ana sa ran bukatun kayayyakin jin kai su karu.  Kuma don a cimma haka, sashin yana yana ci gaba da sabunta tsarinsa tare da bayar da babban fiffiko kan abubuwan da aka fi bukata na kayayyaki da kuma karfafa yadda za a rika karbarsu.”