‘‘Yan gudun hijirar Najeriya 44, 000 ne a Kamaru’

A shekaranjiya  Laraba ne Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya ta ce ‘yan gudun hijirar da suka tsallaka daga Najeriya zuwa Kamaru sun kai dubu 44 kamar yadda BBC ta ruwaito. Kakakin hukumar, Leo Dobbs ne ya bayyana hakan, yana mai yin gargadin cewa lamarin ya faru ne sakamakon sabbin hare-haren […]

‘‘Yan gudun hijirar Najeriya 44, 000 ne a Kamaru’
‘‘Yan gudun hijirar Najeriya 44, 000 ne a Kamaru’

A shekaranjiya  Laraba ne Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya ta ce ‘yan gudun hijirar da suka tsallaka daga Najeriya zuwa Kamaru sun kai dubu 44 kamar yadda BBC ta ruwaito. Kakakin hukumar, Leo Dobbs ne ya bayyana hakan, yana mai yin gargadin cewa lamarin ya faru ne sakamakon sabbin hare-haren da ‘yan Boko Haram ke kai wa a arewacin Najeriya.
A cewarsa, a ‘yan makonnin da suka gabata, ‘yan gudun hijira 30,000 ne a sansanin da ke Minawao, amma yanzu kusan kullum sai karuwa suke yi. Ya yi kira a dauki kwakkwaran mataki na murkushe ‘yan kungiyar ta Boko Haram domin mutane su ci gaba da zama a gidajensu.