’Yan gwangwan suna tono motar da ta shekara 67 da nitsewa a Kogi

Bauchi suna wani yunkuri na tono wata tsohuwar tankar daukar mai da ta yi sama da shekara 67 da fadawa cikin kogin garin.

’Yan gwangwan suna tono motar da ta shekara 67 da nitsewa a Kogi
’Yan gwangwan suna tono motar da ta shekara 67 da nitsewa a Kogi

Al’ummar garin Dindima da ke Karamar Hukumar Bauchi suna wani yunkuri na tono wata tsohuwar tankar daukar mai da ta yi sama da shekara 67 da fadawa cikin kogin garin.

Mutane da dama ne dai suka taru domin ganin yadda wadannan al’umma ke kokarin tono motar.

Lokacin da ya je duba yadda lamarin yake, bayan ya ji ana kokarin fito da motar, mai girma Sarkin Dindima Malam Sale Ubandoma ya ce, wannan motar dai ta fadi ne a cikin kogi, inda ya ce shi ma bai san dalilin da ya sa ake tono ta ba, ya ji labari ne ana tonowa shi ya sa ya taso ya zo ya same su.

Sarki Sale ya ce lokacin da motar ta fadi, mutanen da suka fada suna raye lokacin ana gina gadar.

Ya ce ma’aikatan da ke ginin su suka zo da sojoji suka tone motar da ta nitse a cikin yashi.

Kuma suka kawo abin daga mota suka daga domin fito da ita.

“Sun gama tonowa sai suka tsaya a kan washegari za su zo su daga ta. Allah da ikonSa cikin dare kuma sai ruwa ya zo ya mamaye, dole ta sa suka bar ta kuma daga nan ba wanda ya sake zuwa tona ta.”

Ya ce motar da ta fadi babbar tanka ce ta daukar mai kuma ta fadi ne shake da mai a cikinta.

Sarkin ya ce lokacin da hadarin ya faru mutanen sun fita da rai amma ita motar ta ci gaba da nitsewa a cikin yashi, bayan da ruwa ya shanye ta.

Wani mazaunin garin Dindima, Ibrahim Muhammad Dattijo mai shekaru 67 ya ce lokacin da wannan hatsari ya faru a idonsa ya faru kodayake lokacin yana yaro karami, shekarunsa ba su fi bakwai zuwa takwas ba.

Daya daga cikin wadanda ke kokarin tono motar, Muhammadu Dindima, ya ce shi yana harkar sayar da kayan gwangwan ne kuma sun yi niyyar ciro motar ce domin ganin ko za su samu abinci a jikinta.

Ya ce za su yi haka ne saboda rage matsalar da ake samu, wani lokaci in mutane suka shiga sukan samu rauni a jikin tsohuwar motar da ta nitse cikin yashi, karfenta na
ji musu ciwo.

Ya ce suna wannan aiki ne bayan sun hada kai da wani dan kasuwa daga Jihar Kano.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba