’Yan Hisba sun kama mashaya a Jigawa

Dogarawan Hisba a Jihar Jigawa sun kama wasu mutum hudu bisa zargin su da shan kayan maye tare da aikata badala da wasu mata biyu a cikin wata mota a lokacin da suka kai samame a wata mashaya a Dutse.Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa, Ustaz Aliyu Galamawa ya ce jami’an Hisbar sun kai samame […]

’Yan Hisba sun kama mashaya a Jigawa
’Yan Hisba sun kama mashaya a Jigawa

Dogarawan Hisba a Jihar Jigawa sun kama wasu mutum hudu bisa zargin su da shan kayan maye tare da aikata badala da wasu mata biyu a cikin wata mota a lokacin da suka kai samame a wata mashaya a Dutse.
Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa, Ustaz Aliyu Galamawa ya ce jami’an Hisbar sun kai samame ne Gidan John da ake kira Gindin dinya da wata mashaya da ta yi fice mai suna Rafin Sanyi, inda dandazon karuwai ke sheke ayarsu da kuma masu kwankwadar giya.
Malam Galamawa ya ce za su gabatar da wandanda ake zargin a gaban kotu dominsu
fuskanci hukunci kuma hakan ya zama darasi ga masu sha’awar aikata irinsa a nan gaba.
Awata sabuwa hukumar shigi da fice a Jihar Jigawa ta kai samame a kan iyakokin
jihar inda ta kama bakin haure 135 da suka fito daga Jamhiriyar Nijar.
Kwanturolan hukumar Malam Isah Idris Jere wanda ya tabbatar aukuwar haka ya ce hakan na daya daga cikin aikinsu na kamawa da kuma mayar da duk wanda ya shigo kasar nan ta haramtacciyar hanya.
Ya ce sun kame mutum 77 a karamar Hukumar Gumel, inda suka kama mutum 58
a shiyyar Hadeja.
Malam Isah ya kara da cewa a cikin wata uku sun kama mutum 350 da suka shigo jihar ta haramtacciyar hanya kuma sun mayar da su zuwa inda suka fito.
Da yake karin haske Shugaban karamar Hukumar Kazaure Alhaji Abdullahi Mabo ya ce matakin da hukumar ta dauka na korar bakin hauren ya yi daidai domin yawan tashin hankali da jama’a suke fuskanta a kasar nan da gudunmawar bakin hauren.
Ya ce saboda ana samu sakaci daga hukumomin tsaro an bar komai kara-zube a kasar nan ya sa mutane ke shigowa kasar nan su zauna shekara da shekaru ba da wata takardar izini ba.