’Yan Hisba sun kama matashin da ya damfari tsoho a Jigawa

Dubun wani dan damfara ta cika a daidai lokacin da ya fada hannun dakarun Hisba na Jihar Jigawa, a lokacin da suka kai samame unguwar Maidile da ke Jihar Kano, suka kamo wani matashi da ya sauya murya yana cewa wai shi aljani ne, yana damfarar jama’a, yana raba su da kudinsu.Matashin mai suna Nafi’u […]

’Yan Hisba sun kama matashin da ya damfari tsoho a Jigawa
’Yan Hisba sun kama matashin da ya damfari tsoho a Jigawa

Dubun wani dan damfara ta cika a daidai lokacin da ya fada hannun dakarun Hisba na Jihar Jigawa, a lokacin da suka kai samame unguwar Maidile da ke Jihar Kano, suka kamo wani matashi da ya sauya murya yana cewa wai shi aljani ne, yana damfarar jama’a, yana raba su da kudinsu.
Matashin mai suna Nafi’u Muhammed, dan shekara 25 ya samu nasarar damfarar wani tsoho dan shekara 60, wanda ke zaune a Unguwar Jidawa da ke yankin karamar Hukumar Dutse.
Dattijon  mai suna Sabo Adamu Jidawa, ya ce matashin ya karbi har Naira N220,000 daga hannusa da nufin zai buga masa daloli, wadda zai rika gina masallatai da wuraren ibada, yana taimakon Musulmi.
Da yake karin haske ga manema, labarai Sabo ya ce bai fahimci damfara ba ce sai da karfinsa ya kare, ya fara sayar da kadarorinsa, shi ne wani amininsa ya ankarar da shi cewar wancan mutum ba ba fa aljani ba ne. Daga nan ne suka kai rahoto ga jami’an Hisba wajen gano dan damfararfar.
Ya kara da cewa, a lokacin da suka fara waya da mai damfarar, ya umarce shi da ya yi sadakar dabino, har ta kai ya fara sadakar abinci; ya sa shi ya yi sadakar kaji tara. Daga nan ne ya sa ya kai masa Naira dubu 90, kafin daga bisani asirinsa ya tonu.
A nasa bangaren, shugaban rundunar Hisba ta Jihar Jigawa, Ustaz Aliyu Galamawa ya ce mutumin da suke tuhuma ba karamin dan damfara ba ne, don haka za su ci gaba da tuhumarsa har sai sun gano ko su wane ne ke da hannu wajen aikata laifin, kafin su gabatar da shi gaban kotu.

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato