’Yan Hisba sun kame karuwai 21 a Jigawa
Jami’an Hisba a Jihar Jigawa sun kame karuwai 21 a kokarin da suke yi na raba da karuwan da ake zargi suna kwararowa daga wasu jihohin kasar nan zuwa jihar.Bayanai sun nuna cewa yanzu haka karuwai daga jihohin Kano da Bauchi da Legas sun tare a kauyen Larabar Tambarin Gwani da ke karamar Hukumar Dutse […]
SONY DSC

Jami’an Hisba a Jihar Jigawa sun kame karuwai 21 a kokarin da suke yi na raba da karuwan da ake zargi suna kwararowa daga wasu jihohin kasar nan zuwa jihar.
Bayanai sun nuna cewa yanzu haka karuwai daga jihohin Kano da Bauchi da Legas sun tare a kauyen Larabar Tambarin Gwani da ke karamar Hukumar Dutse da Chaichai da ke karamar Hukumar Ringim, inda suke gwagwajewa tare da makadan da ke yi musu kidan garaya a gidajen da suke karuwanci.
Shugaban Hukumar Hisba na Jihar Malam Aliyu Sa’adu Galamawa ya tabbatar da kamen karuwan, inda ya ce hukumar ta samu bayanai cewa ana aikata badala a gidajen karuwan.
Ya ce a lokacin da hukumar ta kai samame kauyen Chaichai ta kame karuwai takwas da wani tsoho da samari biyu da kuma kayan caca da na kidan garaya a gidan da karuwan suka kama dakuna suna karuwanci.
Ya ce tuni suka mika su ga ’yan sanda wadanda suka gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Dutse inda Mai shari’a Aliyu Muhamma Abdullahi Hadeja ke shari’a.