’Yan Hisbah sun kama mace da namiji suna lalata a tashar mota a Zamfara
Kowanne daga cikinsu na cika bakin ya fi dayan rashin kunya
Jami’an Hukumar Hisbah a jihar Zamfara sun kama wasu matasa mace da namiji suna lalata a cikin motar haya a wata tashar mota da ke Gusau, babban birnin jihar.
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa an kama mutanen ne suna lalatar a bainar jama’a ba tare da la’akari da idon mutane ba.
- Zuwaira Ahmad: ‘Yar shekara 13 da ta rubuta Alqur’ani da ka
- Shin da gaske Ado Gwanja na bata tarbiyyar matasa?
Sai dai ganin haka ne ya sa fasinjoji da hukumomin kamasho na tashar suka ankarar da ’yan Hisban, wadanda su kuma ba su yi wata-wata ba wajen cika hannu da su.
Wani jami’i a hukumar ta Hisbah da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa kafar ta PRNigeria cewa mutanen sun ci gaba da aikata badalar har sai da ’yan Hisbar suka isa wajen.
A cewar jami’in, “Tun da farko dai mutanen biyu sun yi musu a kan wanda ya fi lalacewa da rashin jin kunyar jama’a a tsakaninsu. Inda kowa yake cewa ya fi dayan.
“Ana cikin haka ne sai suka yanke shawarar saduwa a bainar jama’a, sannan suka tube kayansu suka fara lalatar a cikin tasha,” inji majiyar.
A wani labarin kuma, rahotanni sun nuna cewa tuni jami’an hukumar ta Hisbah a jihar ta Zamfara suka gurfanar da mutanen a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kankuri a Gusau, domin su girbi abin da suka shuka.
“Tuni Hisbah ta gurfanar da su a gaban kotun shari’ar Musulunci, kuma da ita za a yi amfani wajen yanke musu hukunci saboda aikata zina. Hakan ya saba da koyarwar addinin Musulunci da ma al’adun mutanen jihar,” inji majiyar.
Aikata zina dai laifi ne a bisa kundin dokokin shari’ar Musulunci na jihar Zamfara.