’Yan ina-da-kisa sun kashe kansila a Fatakwall

Wasu da ake kyautata zaton ’yan ina da kisa ne, sun kashe Honarabul Sotonye Melford Georgewill, kamsilan jam’iyyar APC a mazaba ta biyu da ke karamar Hukumar Akuku Toro ta Jihar Ribas. Makasan sun iske marigayin ne a kofar gidan kakansa da misalin karfe goma na safe, inda suka far masa, suka soke shi da […]

’Yan ina-da-kisa sun kashe kansila a Fatakwall

Wasu da ake kyautata zaton ’yan ina da kisa ne, sun kashe Honarabul Sotonye Melford Georgewill, kamsilan jam’iyyar APC a mazaba ta biyu da ke karamar Hukumar Akuku Toro ta Jihar Ribas. Makasan sun iske marigayin ne a kofar gidan kakansa da misalin karfe goma na safe, inda suka far masa, suka soke shi da abin da ake zato wuka ce kuma nan take ya mutu ko shurawa bai yi ba, sannan suka arce.  Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a ji ko duriyarsu ba.
Gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Ribas ya nuna matukar bakin cikin kisan da aka yi wa kamsila Sotonye Georgewill, kuma ya yi Allah-wadai da aukuwar lamarin.
A ’yan kwanakin nan an ruwaito saboda tsabar adawar siyasa, ’yan siyasa a jihar, wadanda suka ci suka tayar da kai, suna kaurace wa birnin Fatakwal, babban birnin jihar da kuma garuruwansu na asali, sakamakon hari ko kamun a nemi kudin fansa ko kuma dai a nemi halaka su.
Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar ta Ribas Muhammed Ahmed Kaliya game da lamarin ya ce har zuwa lokacin tuntubar, bayanin hakan bai kai gare su ba.