’Yan Indonesiya sun cika buhuna da sulalla sun kai ofishin jakadancin kasar Austiraliya

Masu zanga-zangar adawa da kasar Austiraliya sun cika buhuhhuna da kwabbai da sulalla, inda suka mika su zuwa ga ofishin jakadancin kasar a matsayin mayar da agajin tsunami da kasar ta ba su, saboda gorin da mahukunta a Canberra ke yi cewa, sun taimaka wa kasar, don haka kada a kashe ’yan kasar fataken kwayar […]

’Yan Indonesiya sun cika buhuna da sulalla sun kai ofishin jakadancin kasar Austiraliya
’Yan Indonesiya sun cika buhuna da sulalla sun kai ofishin jakadancin kasar Austiraliya

Masu zanga-zangar adawa da kasar Austiraliya sun cika buhuhhuna da kwabbai da sulalla, inda suka mika su zuwa ga ofishin jakadancin kasar a matsayin mayar da agajin tsunami da kasar ta ba su, saboda gorin da mahukunta a Canberra ke yi cewa, sun taimaka wa kasar, don haka kada a kashe ’yan kasar fataken kwayar nan su biyu.

Masu zanga-zangar sun yi ta ihu, suna kiran sunan Shugaban kasar Austiraliya kan lallai ya rufe musu baki. “Abbott ka nemi afuwa,” a cewarsu, inda suka yi hoton Mista Tony Abott Firayiministan Austiraliya da likakken baki, a daidai lokacin da suke mika kwabban.
A watan da ya wuce ne, Firayiminista Tony Abott ya gorranta wa mahukunta a birnin Jakarta kan taimakon agajin Dala biliyan daya da kasarsa ta bai wa Indonesiya, bayan da kasar ta yi fama da ambaliyar Tsunami, wadda ta haifar da asarar rayuwa, har dubu 22.
Wadannan kalamai ya yi su ne don shawo kan mahukuta a Jakarta kada su halaka fataken miyagun kwayoyin nan ’yan kasar Austiraliya, wadanda ake yi wa lakabi da “Bali Nine,” wato Andrew Chan da Myuran Sukunmaran, wadanda ke jiran wa’adin kisan sun an ba da dadewa ba.
Wannan dabara dai ba ta biya, domin dimbin masu zanga-zanga a Indonesiya sun yi ta tara kwabbai da sulallan kudin kasar, don biyan wadannan kudi da aka yi musu gori a kai. A wata zanga-zangar da aka yi kwananan, wasu dalibai suka cika jakunkunan leda da kudi da sulalla, wadanda kimar darajarsu ta kai rupiah miliyan bakwai, wato Dala 535.