’Yan IPOB sun kashe ’yan Arewa sama da mutum 137 – Bincike
An kashe su ne tsakanin zanga-zangar EndSars zuwa watan Nuwamba 2021.
’Yan A Waren Biyafara (IPOB) sun kashe sama da mutum 137 a jihohin Kudu maso Gabas.
A wani bincike da Aminiya ta gudanar, wasu mahara da ake zaton ’yan IPOB ne a tsakanin zanga-zangar EndSars zuwa watan Nuwamba bana, an gano sun kashe sama da mutum 137 .
A daren Talata shugaban ’yan Arewa mazauna Karamar Hukumar Mbaise, Alhaji Amadu Orlu ya shaida wa wakilinmu cewa, wasu ’yan IPOB sun kashe mutum hudu masu sana’ar sayar da agogo ’yan asalin Jihar Kano mutum biyu kuma suna asibiti kwance ana musu jinya ne da ake kyautata zaton an turo su aiki ne zuwa daya daga cikin jihohin Kudu maso Gabas.
Orlu ya shaida wa Aminiya cewa, daga daren Talata zuwa Alhamis makon jiya mahara da ake zaton ’yan IPOB ne sun kashe wasu ’yan Arewa mutum hudu, biyu kuma na asibiti a garin Okigwe.
Shugaban ya ci gaba da cewa, a garin Umuagwu a Karamar Hukumar Mbaise, ‘yan IPOB sun kashe mutum hudu.
Kazalika ya ce, sun kara kashe wasu mutum uku ’yan kasuwa da ke yawon talla a kauyen Achangale, shi kuma a yankin Karamar Hukumar Obowo da ke Jihar Imo.
Wannan kisan ’yan Arewa da ake yi a Jihar Imo, mazauna jihar ’yan Arewa na ci gaba da nuna takaicinsu tare da bakin cikin irin yadda mahukuntan jihar ke kawar da kai ba tare da daukar matakin hana hakan ba.
Ya kara da cewa, an mayar da rayukan ’yan Arewa a Imo tamkar na kiyashi ko a daren Talata ma an samu karin kisan wasu ’yan Arewa da aka yi wa kwanton bauna aka kashe wasu mutum uku a kauyen Ayara da ke Karamar Hukumar Mbaise.
Majiyar ta tabbatar da karin kisan wasu ’yan Arewa da ake zaton an turo su aiki ne daya daga cikin jihohin Kudu maso Gabas suka tare mota suka fitar da su a marabar Banana a Karamar Hukumar Urlu su ma suka kashe su, jimillar mutum takwas ke nan a dare biyu aka kashe.
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Macheal Attam, domin jin ta bakinsa ya kuma tabbatar da cewa sun samu rahoton faruwar hakan. An yi jana’izar mamatan a Okigwe.