’Yan Izala ba su fushi da ’yan darika sai dai… – Sheikh Jingir
Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce ’yayan kungiyar ba su fushi da ’yan darika, sai dai sukan yi musu wa’azi domin wa’azi yana amfanar masu imani.Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne a Sakkwato lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu, inda […]
Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce ’yayan kungiyar ba su fushi da ’yan darika, sai dai sukan yi musu wa’azi domin wa’azi yana amfanar masu imani.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne a Sakkwato lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu, inda ya ce, “In aka dubi kungiyarmu, wasu jama’a ne suka hadu don kawar da duk wasu abubuwa da ba su cikin Musulunci, bidi’a ce; shirka ce; ko wani aikin laifi, sannan su tsayar da sunnar Annabi Muhammad (SAW),” inji shi.
Sheikh Jingir ya ce Izala kungiya ce ta rayar da al’umma, “Zai ba ni mamaki kwarai wani ya ce muna fushi da su, wannan ba gaskiya ba ne, dukan al’ummar duniya ba wanda muke fushi da shi, soyayyar Musulunci ne ya sa ’yan darika suka shiga cikin sahun wadanda muke yi wa wa’azin su nisanci shirka da tabbatar da tauhidi da nisantar miyagun dabi’u, don haka mu masu wa’azi ne, ba mu fushi da su,” inji Jingir.
Da Aminiya ta tambaye shi maganar hadewar kungiyar da kuma wadanda suka ware, sai ya ce har yanzu kungiyar a hade take, domin a can shi ke jagorantar bangaren Jos, Sheikh Yusuf Sambo na jagorantar Kaduna da suka hade sai aka ce ya jagoranci harkar wa’azi da karantarwa da makamantansu na kungiyar, shi kuma ya zama mataimakinsa, “Sai muka ci gaba da tafiya, yanzu ma da na zo Sakkwato ga ni ga shi, don haka ina da hujjar cewa muna nan a hade, kuma tun bayan da aka hadu a Kaduna aka ce an hade, ba a ji inda aka sake gangami aka ce an rabu ba. To sai ga shi yanzu ana fadin wasu na kokarin mayar da tafiya baya. Wane shiri muke yi kansu, to, a sanina haduwa na nan a majalisar malamai, wasu ko da aka sa su rike wasu ayyuka na kungiya saboda ba su saba da aiki ba, suka kasa zuwa a yi aiki da su, ba su iya taba haduwar baki daya, amma fa ba a bari a kwashe duka, dole a samu wadanda ransu ba ya son yawan wannan aikin da muke yi, wani na son ya dan je ya yi abinsa a gefe da sunan Izala. Kuma za mu rika yi musu wa’azi da tunatar da su, har su fahimta,” inji shi.
Sheikh Jingir Sani ya je Sakkwato ne don ziyara tare da bude wani katafaren masallaci da Malam Altine Maikilishi ya gina.