’Yan Jamhuriyar Tsakiyar Afirka fiye da dubu dari na gudun hijira a Kamaru

Fadace-fadacen da ake yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun sa ‘yan kasar da dama sun kaurace wamatsugununsu.A wata sanarwada Majalisar dinkin Duniya ta wallafa, ta bayyana cewa tsakanin watan Disamba bara zuwa wannan watan da muke ciki, mutane fiye da dubu dari da talatin ne ke gudun hijira a Kamaru. Daga cikinsu akwai musulmai  […]

’Yan Jamhuriyar Tsakiyar Afirka fiye da dubu dari na gudun hijira a Kamaru

Fadace-fadacen da ake yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun sa ‘yan kasar da dama sun kaurace wa
matsugununsu.
A wata sanarwa
da Majalisar dinkin Duniya ta wallafa, ta bayyana cewa tsakanin watan Disamba bara zuwa wannan watan da muke ciki, mutane fiye da dubu dari da talatin ne ke gudun hijira a Kamaru. Daga cikinsu akwai musulmai  su kimanin dubu ashirin wadanda akasarinsu ke tsugunne a gabashin Kamaru, mai makwabtaka da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Kashi daya
cikin hudu na ‘yan gudun hijiran  kuma mata ne da
kananan yara wadanda  basu huce shekaru hudu da haihuwa ba, a bisa ga kididdigar da Hukumar Majalisar dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijira ta yi.
Hukumar ta kuma ce duk kokarin da take yi na wadata ‘yan gudun hijiran da kayayyakin agaji, shirin nata na fuskantar kalubale iri-iri saboda yadda ‘yan gudun hijiran ke kara yawa a kullum.
Akwai rahotannin
da ke cewa wasu dubbannin ‘yan gudun hijiran ma, na rayuwa ne a kwararo-kwararo da karkashin bishiyoyi
saboda karancin muhalli. John Irwin wani jami’in  Hukumar agajita (Doctors without Borders) ya koka da irin halin
da ‘yan gudun hijiran ke ciki. Matsaloli kamar su karancin ruwa da abinci, da kuma rashin kyakkyawan muhalli. Ya kuma ce za su ci gaba da bada  nasu taimakon, a karshe kuma ya bukaci  hukumomi da su taimaka wa ‘yan gudun hijiran.