’Yan Jam’iyyar APC sun nemi gafarar Lamido a Kazaure

Dubban ’ya’yan Jam’iyyar APC na masarautar Kazaure sun tarbi tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido a gadar Kazaure a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da ya je yankin domin yi wa tsohon daraktan shirye-shirye na Gidan Gwamnatin Jihar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa.Majiyarmu ta ce dubban mutanen da suka tarbi Alhaji Sule Lamido sun […]

’Yan Jam’iyyar APC sun nemi gafarar Lamido a Kazaure
’Yan Jam’iyyar APC sun nemi gafarar Lamido a Kazaure

Dubban ’ya’yan Jam’iyyar APC na masarautar Kazaure sun tarbi tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido a gadar Kazaure a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da ya je yankin domin yi wa tsohon daraktan shirye-shirye na Gidan Gwamnatin Jihar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa.
Majiyarmu ta ce dubban mutanen da suka tarbi Alhaji Sule Lamido sun rika cewa “Mun tuba Baba, ka yafe mu mun ci amanarka mun yin zaben tumun-dare, kuma mun gani a kwaryarmu ba za mu sake amincewa da irin wannan ba za mu nuna maka mu ’ya’ya ne idan zaben kananan hukumomi ya zo.”
Majiyar ta ce motoci 15 na wadanda suka tarbi tsohon Gwamnan dukansu ’ya’yan Jam’iyyar APC ne, kuma majiyar ta ce sun je tarbarsa saboda ba a ba su mukamai ba kamar yadda aka yi musu alkawari a lokacin yakin neman zaben Gwamna Abubakar Badaru.
daya daga cikin wadanda suka koma wajen tsohon Gwamnan ya ce yanzu sun fahimci gaskiya gwamnati ba ta yi musu adalci tana debo wadanda ba su bauta wa jam’iyyar ba tana ba su mukamai. Matashin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce sun shirya wa zaben kananan hukumomi da gwamnatin jihar ke shirin yi, inda ya ce jama’a ba za zabi APC domin ta ba su kunya ta kasa cika alkawuran da ta dauka musu, ta bar su suna fama da rashin aiki da talauci.
Sai dai a martanin da Kakakin Gwamnan Jihar Bello Muhammed Zaki ya mayar ya musanta cewa magoya bayan APC ne suka tarbi tsohon Gwamnan, inda ya ce jama’ar Kazaure ihu suka rika yi masa suna barawo ba sa yi.
Ya ce babu dalilin da zai sa mutumin masarautar Kazaure zai yi tarbar kirki ga tsohon Gwamna Sule Lamido in dai ba butulu ba, domin Gwamna Abubakar Badaru ya ba su duk abin da ake yi wa kowane sashi na siyasa. “Ya ba su kwamshina biyu, ya yi musu mashawarta biyu, kuma ya yi musu kananan masu ba Gwamana shawara biyu, don haka yaya za a yi mutumin Kazaure ya yi wa Badaru butulci alhalin duk nade-naden da ake bukata ya yi mana,” inji Zaki. Ya ce waccan magana da ake bazawa ba za ta wuce yarfe irin na ’yan adawa ba, kuma ana yi ne kawai domin a kawo cikas a cikin tafiyar Gwamna Badaru amma ba domin Gwamnan ya gaza ba.