’Yan jam’iyyarmu ne suka jefi Shugaba Jonathan a Bauchi – Bappah Disina

Alhaji Bappah Haruna Disina tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ne kuma shi ne shugaban kwamitin yayata manufofin gwamnatin Malam Isa Yuguda a cikin tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci game da abubuwan da suka faru a lokacin ziyarar Shugaba Jonathan da aka jefi tawagarsa: Me za ka ce game da abin da ya faru […]

’Yan jam’iyyarmu ne suka jefi Shugaba Jonathan a Bauchi – Bappah Disina
’Yan jam’iyyarmu ne suka jefi Shugaba Jonathan a Bauchi – Bappah Disina

Alhaji Bappah Haruna Disina tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ne kuma shi ne shugaban kwamitin yayata manufofin gwamnatin Malam Isa Yuguda a cikin tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci game da abubuwan da suka faru a lokacin ziyarar Shugaba Jonathan da aka jefi tawagarsa:

Me za ka ce game da abin da ya faru a wajen taron kamfe na Shugaba Goodluck Jonathan?
Disina: Magana ta gaskiya ita ce dan jam’iyyar adawa ta APC ba zai zo wurin taron PDP ba. Kamar yadda Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya fada ne cewa ’yan PDP ne suka yi jifa a wajen taron wannan magana gaskiya ce. Wadanda suka yi wannan aika-aika kayan PDP ne a hannunsu kuma hotunan ’yan PDP ne a jikinsu. Saboda haka babu wani dan APC da ya zo wajen domin tada zaune-tsaye. Sai dai kuma akwai wadanda har yanzu ba su yarda da shugabancin wannan jam’iyyar ba a wannan jiha ta Bauchi. Akwai wasu daga cikin ’ya’yan Jihar Bauchi da ke zaune a Birnin Tarayya, Abuja da suke neman cin mutuncin Gwamna Isa Yuguda. Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ba ya da hannu wajen wannan hayaniya ta lokacin ziyarar Shugaba Jonathan. Akwai wadanda suke tura matasa gidan rediyo domin cin mutuncin mutane kuma abin da suke aikatawa ya saba wa doka. Kowa ya san wanda yake haddasa rikici a Jihar Bauchi kuma yana neman raba PDP ne gida biyu. Ba ma zargin Ahmadu Mu’azu sai dai kowa ya san wanda muke zargi wanda yake amfani da matasa wajen tada zaune-tsaye Minista ne a wannan gwamnati. Ya kamata mutane su gane cewa akwai abin da ya fi kudi shi ne mutunci. Kafin Shugaban kasa ya zo an yi ta mitin da matasa wanda kuma ba jam’iyya ba ce ta shirya haka, kuma an yi haka ne domin a ci mutuncin Gwamna a gaban Shugaban kasa. Ya kamata a rika mutunta shugabanci, Alhaji Ibrahim Yaro-yaro shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi kuma ya zamo wajibi a kan duk wani dan jam’iyya ya yi masa biyayya dbakin gwargwado.
Mene ne sakonka ga matasa ’yan siyasa?
Babban sakona ga matasa shi ne don Allah kada wani matashi ya bari wasu ’yan siyasa marasa kishin kasa su yi amfani da shi wajen tada zaune-tsaye a tsakanin al’umma, saura kwanaki kadan a gudanar da zabe. Shugaban kasa ya fi kowa sanin wanda yake haddasa rigima a wannan jam’iyya ta PDP a Bauchi. Wannan rigima daga Abuja ta samo asali kamar yadda Gwamna ya fada a lokacin da yake zantawa da manema labarai. Kafin Shugaban kasa ya zo Bauchi, Gwamna Yuguda ya tara mu game da zuwan mun ba shi shawarwari game da yadda za a gudanar da taron lami lafiya. Mutumin da yake ba ka abinci ka sa an zo an ci mutuncinsa a cikin garin Bauchi saboda haka abin da ya yi kamar ya raba jam’iyyar ne. A matsayina na tsohon dan siyasa ina kira ga ’yan siyasa su guji tada zaune-tsaye. Kuma an yi haka ne domin nuna wa Shugaban kasa cewa Gwamna Yuguda ba ya da kowa a Jihar Bauchi, amma kowa ya san cewa an yi amfani da yara ne marasa tarbiyya. Ya kamata kowa ya shafa wa kansa ruwa, saboda babu wani dan siyasa da yake amfani da ’ya’yansa a lokacin yakin neman zabe.
Ana zargin Gwamna Yuguda ba ya tallar Shugaba Jonathan idan ya je kamfen, me za ka ce?
Yanzu ne muke tsare-tsaren fita kamfen kuma ita siyasa ’yar lissafi ce idan ka duba Jihar Bauchi babu abin da muka samu daga wajen Gwamnatin Tarayya. Yau shekara da shekaru aikin madatsar ruwa ta Kafin Zaki an kasa kammala ta. Kuma babu wani shugaba da ya isa ya tilasta wa masu zabe yin abin da ba sa so. PDP ta riga ta tsaida ’yan takara, kuma wajibi ne a kan duk dan jam’iyya ya yi biyayya ga uwar jam’iyya.
Mene ne sakonka ga ’yan siyasa masu neman mulki ido rufe?
Dukkan wadanda suke neman mulki ido rufe tabbas sun jahilci Allah, saboda Allah ne Yake ba da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya ga dama kowa idonsa a bude yake yanzu. ’Yan jam’iyyarmu ta PDP ne suka jefi Shugaban kasa ba ’yan adawa ba.Ina fatar Allah Ya sa a gudanar da wannan zabe lafiya kuma a kammala lafiya ba tare da tashin hankali ba.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya