‘Yan jarida 10 da ke aiki a ofishin gwamna sun kamu da coronavirus

Ya zuwa yanzu kimanin ‘yan jarida  goma da ke aiki a ofishin gwamnan jihar Akwa-Ibom ne ake zargi suna dauke da cutar coronavirus. Hakan na zuwa ne a  daidai  lokacin da fadar gwamnatin jihar ta qaryata rahoton da ke cewa mutum tara  cikin  mukarraban gwamnatin na dauke da cutar. Makwanni biyu da karyata hakan sai […]

‘Yan jarida 10 da ke aiki a ofishin gwamna sun kamu da coronavirus

‘Yan jaridu

Ya zuwa yanzu kimanin ‘yan jarida  goma da ke aiki a ofishin gwamnan jihar Akwa-Ibom ne ake zargi suna dauke da cutar coronavirus.

Hakan na zuwa ne a  daidai  lokacin da fadar gwamnatin jihar ta qaryata rahoton da ke cewa mutum tara  cikin  mukarraban gwamnatin na dauke da cutar.

Makwanni biyu da karyata hakan sai wasu  rahotanni   ke  nuni da cewa an samu mutum goma ‘yan jarida dake aikin daukar labarai a ofishin gwamnan anyi musu gwajin cutar coronavirus  an kuma  same su  da ita,lamarin da ya jefa kungiyar ‘Yan jarida da al’ummar gari cikin firgici.

Idan za’a iya tunawa cutar  ta lakume wani likita a jahar da ke aikin kula da wadanda coronavirus ta kama.

Wani  dan jarida mai suna Etorobong Inyang na jaridar Edge News ya aike da sako a shafinsa na Facebook cewa an gayyaceshi asibitin kwararru na Ibom domin a tabbatar masa ya kamu da cutar coronavirus.

A nata bangare  Uwargida Idongisit Ashemere shugabar kungiyar wakilan kafafen yada labaru cewa tayi “Nima an kira ni ta wayatar  salula an bukace ni da in miqa kaina asibitin qwararru na Ibom aka tabbatar min cewa mutum goma ‘Yan jarida sun kamu da cutar kurona” inji ta.

Ya zuwa lokacin hada  wannan rahoto  Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa reshen  jihar Akwa Ibom ba ta ce uffan ba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos