’Yan jarida 4 sun rasu a hadarin mota a Akwa Ibom

’Yan jarida hudu da ke aiki a Kamfanin Buga Jaridar The Pioneer mallakar Jihar Akwa Ibom sun rasu nan take a wani mummunan hadarin mota da suka yi a ranar Laraba makon jiya, lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga bikin auren daya daga cikin abokin aikinsu. Bayanin da wakilin Aminiya ya samu […]

’Yan jarida 4 sun rasu a hadarin mota a Akwa Ibom

’Yan jarida hudu da ke aiki a Kamfanin Buga Jaridar The Pioneer mallakar Jihar Akwa Ibom sun rasu nan take a wani mummunan hadarin mota da suka yi a ranar Laraba makon jiya, lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga bikin auren daya daga cikin abokin aikinsu.

Bayanin da wakilin Aminiya ya samu hadarin ya faru ne da yammacin Larabar daidai kan titin Iyafal da ke Uyo daf da shiga gari. An ce mamatan sun je kauyen Ekpene Ukim ne da ke Karamar Hukumar Uruan don halartar bikin auren abokin aikinsu.

Sai dai daya daga cikin ’yan jaridar da hadarin motsar ya rutsa da su kuma ya tsira inda yake jinya a Babban Asibitin Uyo, mai suna Ituk Mbang, ya ce, “Direbanmu yana mugun gudu kamar wanda aka biyo shi kuma a kokarin kauce wa wani rami ne sai motar ta kwace ya kasa shawo kanta daga  sai ta fara juyawa.”

An kai gawarwakin mamatan dakin aje gawa na Babban Asibitin Uyo.

Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Akwa Ibom ta nuna alhininta kan rasuwar ’yan jaridar a cikin wata sanarwa da Sakataren Kungiyar na Jihar, Dominic Akpan ya fitar, inda ya bayyana matukar kaduwar kungiyar tare da mika ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da kuma kamfanin jaridar.