’Yan jarida 6 sun mutu a kusan lokaci guda a Kalaba
’Yan jarida shida ne suka mutu a kasa da mako shida a Jihar Kuros Riba, lamarin da ya haifar da firrgici da tsoro a tsakanin mutane musamman manema labarai a fadin jihar. Hakan ya sa wadansu daga cikin wakilan kafafen watsa labarai da ke aiki a jihar suka bukaci a gayyato malaman addinai su kawo […]
’Yan jarida shida ne suka mutu a kasa da mako shida a Jihar Kuros Riba, lamarin da ya haifar da firrgici da tsoro a tsakanin mutane musamman manema labarai a fadin jihar. Hakan ya sa wadansu daga cikin wakilan kafafen watsa labarai da ke aiki a jihar suka bukaci a gayyato malaman addinai su kawo daukin yin addu’a.
Uku daga cikin ’yan jaridar na aiki ne da kamfanin buga jaridar Nigeria Chronicle mallakar gwamnatin jihar wadanda suka mutun kuwa su ne Unimke Columbus Nawa wanda a da ya taba jan ragamar shugabancin Kungiyar ’Yan jarida (NUJ) ta Jihar Kuros Riba, kana kuma shugaban kamfanin Jaridar Chronicle. Sai Effiong Otu da Joe Agba da kuma Stebe Onoh.
Mutuwar tasu ta auku ne jim kadan bayan ta Ndoma Akpet tsohon shugaban Kungiyar ’Yan jarida ta Jihar Kuro Riba da ke aiki da Hukumar Rediyo da Talabijin malakar gwamnatin jihar. Matamatan sun gamu da ajalinsu ne bayan fama da rashin lafiya a lokuta daban-daban.
Yanzu haka Shugaban Kungiyar ’Yan jarida ta Jihar Kuros Riba (NUJ, Bictor Udu ya kafa kwamitin da zai yi shirye-shiryen binne gawar tsohon Shugaban Kungiyar wanda daga hannunsa ya karbi ragamar kungiyar shekara hudu baya.
Kwamitin shirye-shiryen jana’izar na karkashin jagorancin Mazi Juded Okoro