’Yan jarida na bata sunan gwamnatina – Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya soki lamirin wasu ’yan jarida da ke aiki a jihar bisa yadda suke bata sunan gwamnatinsa, inda ya ce ’yan jarida wakilai ne tsakanin gwamnati da jama’a amma maimakon su yi aikinsu na wayar wa jama’a kai sai suka rika gurbata tunanin al’umma da labaran karya.Gwamna Lamido ya […]

’Yan jarida na bata sunan gwamnatina – Lamido
’Yan jarida na bata sunan gwamnatina – Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya soki lamirin wasu ’yan jarida da ke aiki a jihar bisa yadda suke bata sunan gwamnatinsa, inda ya ce ’yan jarida wakilai ne tsakanin gwamnati da jama’a amma maimakon su yi aikinsu na wayar wa jama’a kai sai suka rika gurbata tunanin al’umma da labaran karya.
Gwamna Lamido ya ce mafi yawan ’yan jaridar da ke aiki a jihar ba sa fadar labarin ayyukan alherin da yake yi sai dai wadanda za su bata gwamnatinsa inda ya kawo misali da labarin an jefe shi a Hadeja alhalin ba gaskiya ba ne, aka zo aka ce wai ya cire wani limami daga limanci kuma aka je daji aka dauko hotunan yara suna karatu a gindin bishiya don a nuna wa duniya daliban jihar a karkashin bishiya suke daukar darasi don kawai a bata gwamnatinsa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin shan ruwan da ya shirya wa manema labarai da ’yan siyasa a Dutse.
Ya shawarci manema labarai su canja halayensu na bayar da labarai na bata gwamnati, su koma ga fadar labarai na alheri da suke cike da gaskiya da za su amfani jama’a.